Ramadan: Wata Cocin Kaduna Ta Raba Buhuhunan Hatsi Ga Musulmai Don Inganta Dangantakar Dake Tsakaninsu

0
421

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WATA Cocin Christ Evangelical Intercessory and Life Intervention Ministry da ke Sabon Tasha a Jihar Kaduna ta bayar da gudummawar buhuhunan hatsi iri daban-daban guda 500 ga al’ummar Musulmi a lokacin da suke shirye-shiryen gudanar da azumin watan Ramadan na bana.

Majami’ar ta bayyana cewa an yi amfani da raba nau’in hatsin iri daban-daban ne domin kara samar da zaman lafiya, hadin kai, juriya, soyayya da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinan biyu.

Babban mai kula da cocin, Fasto Yohana Buru ya jagoranci tawagar cocin zuwa babban masallacin Juma’a na titin Kano Road a safiyar Juma’a domin bayar da tallafin kayan abinci ga ’yan masallacin.

Ya shaida wa shugabannin masallacin cewa a raba hatsin ga talakawa musulmi, da mabaratan tituna, da marasa galihu da kuma zawarawa.

A cewar sa, an yi hakan ne domin baiwa wadannan Musulman da aka gano domin su samu isasshen abinci a lokacin azumin na kwanaki 30.

Don haka, ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya kawo mana karshen matsalolin rashin tsaro da kasar nan da ake fuskanta, musamman a Arewacin kasar nan.

“Wannan shi ne karo na 6 da cocin ke raba buhunan hatsi da sauran kayan abinci ga dimbin mabarata a kan tituna, da ‘yan gudun hijira, da kananan yara a gidajen marayu da kuma talakawa musulmi a cikin al’umma.”

A cewar malamin, “Ramadan din bana na zuwa ne a cikin matsalolin rashin tsaro, tsadar kayan abinci, karancin man fetur, da sauran kayan dafa abinci kamar itacen wuta da gawayi a Jihohin Arewa 19.

An ruwaito cewa Cocin ta raba hatsi, da kayayyakin addu’o’i ga sama da daruruwan musulmi marasa galihu da mabukata wadanda suka hada da matan da mazajensu suka mutu.

‘Dole ne mu tuna cewa mu iyali ɗaya ne a ƙarƙashin Allah, muna bauta wa Allah ɗaya, kuma mun fito daga zuriyar Adamu da Hauwa’u, saboda haka dole ne mu haɗa hannu don tallafa wa juna a kowane yanayi.”

Malamin ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su rika tunawa da marasa galihu, talakawa, ‘yan gudun hijira da kuma matan da mazansu suka rasu a cikin al’umma domin su samu damar gudanar da Azumin wannan kwanaki 30 cikin sauki.

Leave a Reply