Yaƙin Ukraine: Janar-Janar Na Rasha Da Aka Kashe A Ukraine Zuwa Yanzu

0
740

Daga Wakilinmu

MA’AIKATAR tsaron Ukraine ta ce an kara kashe wani janar na Rasha mai suna Yakov Rezantsev, a wani harin sama a kudancin birnin Kharson.

Rezantsev kwamandan runduna ta 49 ne ta sojojin Rasha.

Jami’an kasashen yamma sun ce shi ne janar na bakwai da ya mutu a Ukraine, kuma na biyu da aka kashe da ke rike da mukamin lafta janar mafi girma.

Ana zaton cewe karancin biyayyar dakarun sojin Rasha ne ya ke tilastawa manyan jami’ai zuwa fagen daga.

Cikin wata tattaunawa da aka yi har da dakarun Ukraine, wani sojan Rasha ya yi koken cewa Rezantsev ya yi ikrarin dole yakin ya kare a cikin sa’o’i, kwana huku kacal bayan fara yakin.

Kafafen sada zumunta na Ukraine a ranar Juma’a sun ce an kashe janar din ne a kusa da Kherson, wani wajen da Rasha ke amfani da shi a matsayin sansanin soji da Ukraine ta kai wa hari sau da dama.

An kara rawaito cewa an kashe wani laftana janar Andrei Mordvichev, a wani harin Ukraine a dao sansanin.

Kherson ne birnin Ukraine na farko da Rasha ta fara mamayewa, duk da cewa akwairahotanni da ke cewa akan samun zanga-zanga a kullum ta nuna kin jinin mamayar Rasha.

Duk da cewa Rasha ta tabbatar da mutuwar janar daya ne kawai, kyiv da jami’an yamma sun yi amannar sun kai bakwai janar din da aka kashe tun daga fara yakin.

Ka zalika an musanta mutuwar Manjo Janar Magomed Tushayev na tawagar kasa ta Chechen.

Ba abu ba ne da aka saba gani irin wadannan manyan jami’an na rasha su fita fagen daga, kuma kasashen yamma sun yi amannar cewa yanayin rashin biyayyar sojojin Rasha ne ya tilasta musu fita.

Turjiyar da dakarun Ukraine suka yi, da kuma kayanki marasa inganci da Rasha ke fama da shi, na daga cikin abubuwan da suka janyo mutuwar mutanen.

Dakarun Rasha sun dogara ne kan yadda harkokin sadarwa ke gudana a bude, misali ta wayar salula da tattaunawar da ake ta wayar jami’ai wadannan na basu damar sanin inda manyan jami’ai suke.

Rasha tace sojojinta 1,351 sun mutu tun daga fara yakin Ukraine, sai dai kasashen yamma sun ce adadin ya wuce haka.

Yakov Rezantsev

Rahotanni sun ce Laftana Janar Yakov Rezantsev an kashe shi ne a wani harin sama da aka kai kusa da garin Kherson.

An masa karin girma ne zuwa lafatana janar a bara, kuma shi ne kwamandan runduna ta 49 da ke lardin kudancin Rasha.

An ce yana cikin wadanda suka halarci yakin Syria.

Andrei Mordvichev

Jami’an Ukraine sun ce an kashe Andrei Mordvichev shi ma a Kherson a wani harin sama.

Shi ne kwamandan runduna ta 8 ta sojojin Rasha da ke yakin kudanci.

An ce an kashe shi ne a ranar 18 ga watan Maris.

Oleg Mityaev graphic

An ruwaito cewa an kashe Manjo Janar Oleg Mityaev a wani wuri kusa da birnin Mariupol, garin da ke kudu maso gabashin Ukraine inda aka ci gaba da kai manyan hare-hare a baya.

Wata tawaga a Ukraine ta yi ikrarin kashe shi.

Shi ne kwamandan tawagar sojin Rasha ta 150 da ke lura da makaman da ke tafiyar da su a motoci, wani sansani da aka bude a 2016, dake a lardin Rostov da ke kusa da iyakar Ukraine.

Ukraine ta yi ikirarin an kafa wannan tawaga ne domin ta shiga yakin da ake yi cikin sauki su mamaye yankin gabashin Ukraine, sai dai Rasha ta musanta hakan.

Andrei Kolesnikov graphic

Manjo Janar Andrei Kolesnikov, na cikin rundunar ta 29, an kashe shi ranar 11 ga watan Maris, kamar yadda majiyoyin Ukraine suka bayyyana.

Ba a fadi ko ta yaya aka kashe shi ba.

Bayan Kolesnikov ya kasance janar din Rasha na uku da aka kashe, daya daga cikin manyan jami’an yamma ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na PA cewa Rasha za su fuskanci matsalar rashin hadin kai daaga kananan dakarunsu tsakaninsu da manya.

Vitaly Gerasimov

Manjo Janar Vitaly Gerasimov, babban jami’i a runduna ta 41 an kashe shi a ranar 7 ga watan Maris a wajen birnin Kharkiv, kamar yadda ma’aikatar tsaro ta Ukraine ta bayyana.

Birnin Kharkiv da ke kusa da iyaka Rasha ya fuskanci muggan hare-haren dakarun Rasha.

Vitaly Gerasimov na cikin yakin Chechen na biyu, dakarun Rasha da suka yi yaki a Syria da kuma mamayar da Rasha ta yi wa Crimea a 2014.

Andrey Sukhovetsky

Sai Manjo Janar Andrey Sukhovetsky, mataimakin kwamandan rundunar da Gerasimov ya fito ne, an ce an kashe shi a ranar 3 ga watan Maris.

Kamar dai Gerasimov, shi ma Sukhovetsky na cikin tawagar da suka yi aiki a Crimea da Syria.

Ba kamar sauran janar din ba, mutuwar Sukhovetsky an sanar da ita a kafafen sada zumunta na Rasha kuma shi ma shugaban Vladimir Putin ya tabbatar da ita a wasu taruka.

Leave a Reply