Sanata Uba Sani Ya Bayar Da Kyautar Mota Ga Kungiyar NUJ Kaduna

0
382

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

DAN takardar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin Jam’iyyar APC, Malam Uba Sani, kuma Sanata mai ci dake wakiltar Jihar Kaduna ta tsakiya a zauren majalisar dattawa a ranar Laraba ya bayar da kyautar mota ga kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna..

Sanatan Uba Sani, daya samu wakilcin babban Jami’in mazabarsa na shiyya, Abubakar Rabi’u Abubakar, ya bayyana cewa an bayar da motar mai kirar salun ne domin inganta al’amuran da harkokin sufuri na cibiyar Kungiyar wajen tabbatar da isar da aikinsu na tattarawa da yada bayanai ga jama’a.

Ya ce makasudin samar da motar ga cibiyar Kungiyar NUJ Kaduna, ya samo asali ne daga doguwar alaka da yake da ‘yan jaridu.

“Wannan gudummawar ita ce hanyarmu ta bayar da tamu gudunmawar don taimakawa wajen yada labarai masu inganci da gaggawa daga Kungiyar, da kuma tsara al’amuran jama’a ta hanyar wayar da kan jama’a don sanin hakikanin abin da ke faruwa a harkokin mulki a Kaduna,” inji shi.

Sani ya kuma kara da cewa an bayar da tallafin ne domin zaburar da mata ganin cewa kungiyar Kaduna na da mace a matsayin shugabar farko da ke gudanar da harkokin cibiyar Kungiyar.

“Kamar yadda kuka sani, ni da gwamnan Jihar Kaduna, a kodayaushe muna son ganin mata suna rike da mukamai a cikin Gwamnati, suna gudanar da bincike kan al’amuran wurare masu mahimmanci a cikin al’umma.

“Muna matukar sha’awar kafofin watsa labaru, kuma hakan yana sanar da ra’ayinmu game da gudummawar, tare da yin duk damar da za ta halarci ayyukan watsa labarai lokacin da aka gayyace mu.

“Taimakon ya zo daidai da motoci 59 da muka bayar kwanaki biyu da suka gabata don yakin neman zabe, a gaskiya muna da sha’awar ci gaban ’yan jarida, kuma wannan ba shi ne karon farko da za mu bayar da gudunmawa ta wata hanya ko wata ba don samun nasarar su,” inji Sani.

Da take karbar makullin motar, da kuma takardar, shugabar kungiyar NUJ Kaduna, Hajiya Asma’u Halilu, ta godewa Sanatan bisa wannan karimcin.

Ta ce samun motar a matsayin abin hawa ga Kungiyar wata nasara ce kuma hakan zai yi tasiri wajen rage musu zirga-zirga.

“Mun zo ne a lokacin da Kungiyar ba ta da abin hawa kuma yau da yardar Allah Sanata Uba Sani ya ba mu daya,” inji Asma’u

Ta kuma yi addu’ar Allah ya taimaki Sanatan ya cim ma burinsa ya kuma ba shi zuciyar ci gaba da ciyar da al’ummar mazabar sa da ma mabukata baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here