AYCF Ta Ankarar Da Majalisar Dokoki, DSS Bisa Zargin Son Zuciya Na Karin Girman Hukumar Kwastan

0
393

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

SAKAMAKON irin rade- radin da ake yi kuma suna kara bazuwa cewa rundunar hukumar kwastan ta Najeriya na kokarin cire wadansu Jami’anta da aka dauka aiki kafin shekarar 2009 daga jadawalin wadanda za a yi wa karin girma.

Hakan ya sa kungiyar matasa masu tuntuba ta Arewa (AYCF) ke yin kira ga Jami’an Tsaron Yan Sandan farin kaya na DSS da su hanzarta kama aiki a game da wannan batun domin hukumar gudanarwar Jami’an kwastan masu yaki da yan fasa kauri su yi abin da ya dace.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun shugaban kungiyar AYCF na kasa Alhaji Shettima Yerima, wanda aka rabawa manema labarai a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2022.

Ya ce “Muna yin kira ga daukacin majalisar dokoki ta kasa da su hanzarta shiga wannan maganar domin a kwatowa mama’s Hakkinsu, domin ganin wannan lamarin mai sarkakiya da kuma mummunan hadari na yin zabi sonka bai kai lamari ba.

Saboda kasancewar hukumar kwastan mai matukar muhimmanci ga harkokin tsaron kasa, muna ganin cewa hukumar tsaron Yan Sandan farin kaya ta DSS ya dace su kasance a cikin gudanar da wannan al’amarin aikin karin girma ga ma’aikatan kwastan wanda yakasance za a yi masa sakayya ne ga irin abin da suka aikata na yin aiki tukuru”, inji shi.

Kungiyar ta AYCF ta ci gaba da bayanin cewa wannan matakin da suka dauka sun yi ne da nufin ganin an yi wa kowane ma’aikaci adalci a wajen batun karin girma a duk lokacin da hakan ya taso,

“Mun samu tattara bayanai cewa an shirya za a cire wadansu mutane ne a wajen batun yin karin girman musamman wadanda aka dauka aikin kwastan daga shekarar 2009 da 2015.

“Hakika yin irin hakan ba dai dai ba ne domin akwai ma’aikatan wannan hukumar da suka dade suna yin aiki na tsawon shekaru da yawa har masu shekaru 30 akwai”.

“Wannan matakin da hukumar kwastan ke dauka na nuni ne da cewa mahawarar da ake ta tafkawa a game da yadda ba a samu damar daukar wasu sababbin ma’aikata ba daga shekarar 1992 da 1994, har sai a 2009 lokacin da Gwamnatin Goodluck Jonathan da janye dokar hana daukar sababbin ma’aikata”, kamar yadda suka ce.

Kungiyar AYCF ta ce bisa dogaro da irin sahihan bayanan da ta samu, sun cimma matsaya kamar haka da suke fatan za a duba sosai da idanun basira;

  1. Cewa irin gibin da aka samu sakamakon tazara mai tsawo dalilin Sanya dokar yin hani a dauki ma’aikata, ba laifin ma’aikatan hukumar kwastan ba ne da suka bayar da duk wata damar da suke da ita tun daga karfi, tunaninsu da jinin jikinsu a wajen gudanar da aikin domin kasa ta ci gaba har na tsawon shekaru sama da Talatin (30).
  2. Saboda haka bamu amince da hakan ba domin babu wanda zai yarda da hakan sam sam, duk wani tsarin da za a yi amfani da shi wajen yi wa jami’an hukumar kwastan katin girma ba dai ta bayan gida ba dole ne abi doka da ka’ida kawai.

3.Mun yi tsammanin cewa tsarin ganin mutunci da girmam juna da ya kasance shi ne tsarin shugaba Muhammadu Buhari, wannan ne aka Sani da shi, ya dace ayi amfani da hakan domin tabbatar da an yi wa kowa adalci

4.Hakika hankalin mu ya tashi duk min damu ganin irin yadda wannan hukumar ta kasa bin doka da ka’idar yi wa jama’a karin girm duk da cewa akwai tsarin da tanajin dokar kasa ta tanadar a kan yin hakan amma an yi biris da shi.

  1. Kuma lamari ne abin ban kinya kwarai hukumar kwastan ta rika aiwatar da irin wannan da ya sabawa dokar kasa, ba kuma tare da yin aiki da ofishin ministan kudi da tsare tsare ba, ko kuma neman shawara daga ofishin shugaban ma’aikata na kasa ba ko kuma Sakataren Gwamnatin tarayya ba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here