Daga; Isah Ahmed, Jos.
HUKUMAR zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana Mista Musa Agah na Jam’iyyar PDP, a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi, na kujerar majalisar wakilai ta tarayya ta mazabar Jos ta Arewa da Bassa, da ke jihar Filato da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.
Shi dai wannan zaben cike gurbi da aka gudanar, an gudanar da shi ne sakamakon rasuwar tsohon dan majalisar da ke wakiltar wannan mazaba. Marigayi Alhaji Haruna Maitala, wanda ya rasu a daren ranar Juma’a 2 ga watan Afrilun, shekarar da ta gabata, a wani hadarin mota da ya rutsa da shi, a hanyar Abuja zuwa Jos.
Da yake bayyana sakamakon zaben, a safiyar lahadi, babban jami’in Hukumar zabe ta INEC, da ya jagoranci wannan zabe Dokta Oyeyinka Oyeyinde, ya bayyana cewa Mista Musa Agah na jam’iyyar PDP, ya sami kuru’u 40,343 a wannan zabe da aka gudanar. A yayinda Gwani Adam Alkali na jam’iyyar PRP ya sami kuru’u 37,757.
Har’ila yau ya ce Mista Joseph Abbey na jam’iyyar APC ya sami kuru’u 26,111 a wannan zabe.
Ya ce don haka Mista Musa Agah na Jam’iyyar PDP ne, ya lashe wannan zabe.