Madarasatu Nuruddeen Gudau, Ta Yaye Dalibai 41 Da Su Ka Yi Saukar Alkur’ani

1
422

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

A RANAR 12-2-2022 ne aka yi bikin saukar karatun Alkur’ani mai tsarki na jimlar dalubai 41 watau maza 11, mata 30 a makarantar Islamiyya ta Nuruddeen dake garin Gudau yankin karamar hukumar Dawakin Tofa tare da gabatar da jawabai na kwarin gwiwar neman ilimi da aiki da shi.

Sannan bikin saukar karatun ya sami halartar manyan malamai masu fadakarwa da jami’an gwamnati da kuma iyayen yara inda suka shaida yadda wannan makaranta ke kokari wajen koyar da darussa da kuma tarbiyya ga yara maza da mata.

Tun da farko a jawabin sa, shugaban makarantar malam Sani Idris Dalha Gudau ya bayyana takaitaccen tarihin makarantar da yadda aka fara karatu da yara kalilan domin tabbatar da ganin ana baiwa yaran wannan yanki ilimin addini da kuma na zamani ba tare da nuna gajiyawa ba.

Haka kuma ya sanar da cewa akwai malamai masu matukar kwazo a wannan makaranta ta Nuruddeen Islamiyya wadanda kuma sake da kokari wajen koyar da darussa daidai fahimtar dalubai, sannan iyayen yara suna baiwa makarantar goyon baya da kara wa yaran kwarin gwiwa wanda hakan ta sanya ake yaye dalubai masu nagarta a wannan makaranta.

Malam Sani Idris Gudau yayi amfani da wannan dama inda ya jinjinawa gwamnan jihar Kano Dokta Abdullah Umar Ganduje saboda kokarin da gwamnatin sa keyi wajen bunkasa ilimi a fadin Jihar, tare da assasa shirin bada ilimi kyuta kuma dole wanda hakan abin alfahari ne.

Haka kuma shugaban makarantar ya jinjinawa da wakilin karamar hukumar Dawakin Tofa a majalisar dokokin Jihar Kano, Alhaji Saleh Ahmed Marke da kuma shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwa da kansilan mazabar Gargari Alhaji Abdullah Yahaya Dungurawa saboda kokarin da suke yi wajen kyutata yanayin ilimi a yankin.

Wakilin hakimin Dawakin Tofa, Alhaji Kabiru Ali da wakilin Dan majalisar dokoki Malam Muktar Tattarawa da wakilin shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Abdullahi Yahaya Dungurawa da kuma kansilan walwala da jin dadin jama’a na karamar hukumar Dawakin Tofa Malam Haruna Dan Zaura sun gabatar da jawabai a wajen bikin domin zaburar da iyaye wajen kula da ilimin yayan su.

Bayan gudanar da darasu ga dalubai, wakilin mu ya tattuna da wasu daga cikin daluban da suka yi saukar inda dukkanin su suka yaba wa malamai da iyayen su saboda kokarin da suka yi wajen tabbatar da ganin sun rabauta daga ilimin addini da kuma na zamani ba tare da wata matsala ba.

1 COMMENT

Leave a Reply