Daga; Bashir Bello, Majalisa Abuja.
DAN Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Bagudu Suru ta Jihar Kebbi, Honarabul Bello A. Kaoje, ya bayyana cewa kafa Kwalejin Kiwon Dabbobi a kasar Najeriya wani abu ne wanda zai kara habbaka tallafin arzikin kasa ta yadda za ta kara dogaro da kanta.
A tattaunawarsa da manema labarai jim kadan bayan kudirin sa ya wuce karatu na biyu a Majalisar Tarayya, Honarabul Bello ya shaida cewa samun irin wannan ci gaba a fadin Tarayyar Najeriya wani sila ce wacce za a bunkasa harkokin kiwo da Noma wanda zai tallafawa Kasar.
Ya kara da cewa wannan yunkurin da Majalisar Gwamnatin Tarayyar ke Kokarin yi, abu ne wanda ba ma Kasar Najeriya kadai za ta amfana ba, har ma da kasashen da su ke da makwabtaka da ita, sakamakon cigaban da za a samu, kana zai ba da damar karin samun ayyuka ga al’ummar Kasar.
Ya ce “abu ne wanda duk muka sani cewa Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Gwamnatin Jihar Kebbi sun mayar da hankali wajen ganin an habbaka harkar Noma, shi yasa yin wannan Makaranta zai kara taimakawa wajen ganin an cimma burin da ake da shi a kasar nan da harkar Noma.”
“Sannan tallafin harkar Noma (ATF) da ake son gudanarwa, wani abu ne wanda zai kara habbaka tunanin Gwamnati da harkar Noman ta yadda zai tallafawa duk wani sashen harkar Noma a kasar domin zama da kafafunta da kuma amfani zuwa ga al’umma.”
A karshe, Dan Majalisar Bello Kaoje, ya bayyana cewa samun makarantar irin wannan wata dama ce za ta koya wa al’umma Ilimin Dabbobi, kana zata kawo ci gaba a fannin samun Ilimin Dabbobi da Noma wanda zai bunkasa al’amura da harkoki baki daya.