Daga, Rabo Haladu.
MAJALISAR wakilaii a Najeriya ta buƙaci Gwamnati ta samar da kyamarorin da za a riƙa ɗaurawa a jikin Jami’an tsaro, kuma a kafa cibiyoyin sa ido a kan aikace-aikacensu a faɗin kasarnan.
A cewar majalisar sanya wa jami’an tsaro kyamarori, zai taimaka wajen rage ƙorafe-ƙorafen keta haƙƙin ɗan adam da kuma tozarta ikon da doka ta ba su.
Honarabul Abubakar Yunus, ɗan majalisar wakilai ya kuma shaida cewa dalilin daukar wannan matakin, shi ne yadda korafe-korafe suka yi yawa kan Jami’an ‘yan sandan ta fuskar amfani da karfi fiye da kima ga farar hula.
”Ana son tabbatar da aiki ingantacce, kuma bisa tsari ba tare da wata kumbiya-kumbiya da cuku-cuku irin na jami’an tsaro, wannan shi ne abin da wannan doka ta ke son kawarwa.
Babbandalilin da ya sanya muke so yin hakan a wanna zamani shi ne tuhume-tuhume sun yi yawa kan ‘yan sandan Najeriya, wanda ake ganin su na kisa ba gaira ba dalili, kuma yawanci idan abu ya faru sai ka ji sun ce wai an yi domin tsare kan su,” in ji Honarabul Yunus.
Ya kara da cewa a wasu lokutan za a ga jami’an kwastam sun harbe mutum, ko jami’an ‘yan sanda a wurin binciken ababen hawa su harbe mutum, da dai sauran lamura da ke faruwa irin hakan.
Wadannan na daga cikin dalilan da majalisa ta kawo dokar ta yadda idan suka aikata wanna kamarar da ke jikinsu za ta nadi duk wani motsinsu ta yadda za a san halin da suke ciki a wuraren aiki.
Dalilan sun hada da rikicin Boko Haram, sai kuma ta ‘yan fashin daji, da barayi mutane domin neman kudin fansa, da makamantansu, sai muka lura su jami’an tsaro da za su kare hakkin dan adam ana tuhumarsu da ketawa.
Waɗannan dalili suka sa muka ga dacewar yin hakan sanna baki ya zo ɗaya akan wannan kuduri sannan dukkan majalisa sun amince da shi ba tare da wani ja-in-ja ba.”
Yunus ya ce nan ba da jimawa ba za a fara ganin wannan doka ta fara aiki, kuma an yi nasara ta fado bangaren da majalisa ke bai wa shawara, sannan za mu tabbatar wannan shawara da dokar za ta kai ga kwamitin da ke tabbatar da doka domin ganin an fara amfani da ita ba tare da bata lokaci ba.
Su na kuma fatan ganin da zarar kwamitin ya zauna ya yi nazari akai ba zai dauki lokaci ba za a zartar da shi.
Ko a shekarar 2020 sai da matasan Najeriya suka jagoranci gagarumar zanga-zangar ƙyamatar kisa da cin zalin da ƴan sanda ke yi a Najeriya.