- ‘Daga Rabo Haladu
- Rundunar ‘yan sanda a jihar Borno ta ce tana ci gaba da bincike kan wani ma’aikacin agaji da ta kama bisa zargin ya yi wa wata matashiya ‘yar gudun hijira fyaɗe a Maiduguri.
An kuma yi zargin cewa matashiyar ta kashe kanta bayan faruwar lamarin a unguwar rukunin gidajen 303 ranar Talata.’Yan sanda ne dai suka kai dauki lokacin da suka jiyo ihu da kuma hayaniyar matashiyar ‘yar kimanin shekara goma sha bakwai.Sun ce bayan bude kofa ne kuma sai matashiyar ta fito tana korafin cewa an keta mata matancinta.Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Borno Sani Kamilu Muhammad, ya ce zuwa yanzu bincikensu bai tabbatar musu da cewa ko matashiyarce ta kashe kanta da kanta ba.Jami’in dan sandan ya ce,”Muna bincike a halin yanzu kuma sai abin da binciken ya tabbatar mana sannan zamu mika shi ga kotu domin yin hukuncin da ya dace.
Rundunar ‘yan sandan ta ce shekarun ma’aikacin agajin da ake zargi 35, ita kuma matashiyar bata wuce shekara 18 ba.Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ya ce bisa bayanin da suka samu jami’in agajin saurayin matashiyar ne.Ya ce ”Kamar yadda makwabtan jami’in suka sanar da mu, an ji ihu ne da aka je aka bude kofar gidan jami’in sai ga matashiyar ta fito tana ihu a kan an keta haddinta to daga nan ne sai ta wuce dakin girki ta dauki wuka ta cakawa kanta”To sai dai ya ce,” A halin yanzu bincike ne kawai zai tabbatar da gaskiyar abin da ya faru don yanzu zargi ake yi”.Rahotanni sun ce matashiyar dai na zaune da iyayenta a unguwar Kaleri cikin birnin Maiduguri bayan rikicin Boko Haram ya raba su da garinsu.