Yadda wani mutum ya yi wa agolarsa mai shekara 3 fyaɗe a Jihar Bauchi

0
548

'Yan sandan Najeriya

Daga Rabo Haladu

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi, ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da yi wa agolarsa mai shekara 3 fyaɗe a Unguwar Doya da ke ƙaramar hukumar Kirfi.

Wata sanarwar rundunar ta ce mahaifiyar yarinyar ce ta kai ƙorafi ofishin ƴan sandan yanki, inda ta shaida musu cewa ”Mijina Ali Lawan ya buƙaci na kai masa tabarma don ya kwantar da ita ta yi barci a ranar 9 ga watan nan”.

”Ina komawa ɗakin na tarar da ita magashiyyan tana ta gumi sharaf-sharaf da amai, sannan gabanta ya kumbura yana zubar da jini” in ji mahaifiyarta.

Bayan ta sanar da ƴan sandan ne aka tura jami’ai cikin shiri, waɗanda su kuma suka kai ta babban asibitin ƙaramar hukumar ta Kirfi don samun kulawa.Daga baya dai binciken likitoci ya tabbatar da cewa fyaɗe aka yi wa wannan yarinya da muka zaɓi mu sakaye sunanta.

Sanarwar ƴan sandan ta ce an kama mahaifin nata, kana ana ci gaba da bincike kafin gurfanar da shi a gaban kotu.

Fyade

Ko a kwanakin baya ma sai da aka kama wani mutumi mai shekara 45 da zargin yi wa wata yarinya ƴar shekara 7 fyade a jihar ta Bauchi.

Lamarin ya faru ne a garin Faggo da ke ƙaramar hukumar Shira a jihar ta Bauchi.

Ɗan majalisar da ke wakiltar yankin Honarabul Bello Muazu Shira, wanda ya tayar da batun a majalisar dokokin jihar ya yi kiran a gaggauta kama mutumin kan zargin yi wa ƴar shekara bakwai fyaɗe.

“Ya yi wa yarinyar barazana da makami ya yi mata fyaɗe,” in ji shi

A baya-bayan nan gwamnatin jihar ta Bauchi ta kafa wata doka da ta kira VAPP wadda a turance ake kira Violence Against Persons Prohibition, ta kuma tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da laifin yi wa yara kanana Fyaɗe.

Haka ma dokar ta tanadi ɗaurin rai da rai ga wanda ya yi wa babbar mace fyaɗe, da kuma ɗaurin shekaru 20 ga waɗanda suka yi wa mace daya taron dangi.

Hukumomin ƴan sanda a jihar sun ce sun sha samun rahotannin aikata fyaɗe a jihar.

Mene ne fyade?

Getty Images

Dakta Nu’uman Habib, masanin halayyar dan Adam ne a Jami’ar Bayero da ke Kano ne, kuma a cewarsa, “fyaɗe yana nufin haike wa mata, wani sa’in ma har maza ba tare da izininsu ba, ba tare da sahalewarsu ba, ba tare da yardarsu ba.”

Dakta Nu’uman ya ce tasirin fyaɗe na da girma musamman a rayuwar yara, don kuwa ya kan daɗe a kwakwalwarsu kuma ya jefa su cikin damuwa da tsoro da rashin yarda da amincewa.

“Duk wanda suka haɗu da shi sai su yi tsammanin mai irin wannan halayyar ne. Kuma damuwar takan daɗe tare da su a cikin kwakwalawarsu kusan ta sa ma su sukurkuce”, a cewarsa.

Sai dai bisa alama jama’a ba su gane haka ba, don kuwa ba a cika tattauna batutuwan da suka shafi fyade ba, bare a bai wa wanda a ka yi wa taimakon da ya dace.

Idan aka yi wa wata ko wani fyaɗe, shi da iyalansa sukan zage dantse su tabbatar mutane ba su sani ba. Wannan ba ya rasa nasaba da ƙyama da ake nuna wa waɗanda aka yi wa fyaɗe da iyalansu.

Kuma wannan yana hana jami’an tsaro yin aikinsu yadda ya kamata, musamman ta fannin bincike da yanke hukunci ga wanda ya aikata laifin.

Leave a Reply