An Bukaci Matasa Da Su Kama Sana’ar Noma-Inji Ali Branco

1
378

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

An yi kira ga matasan jihar Kano da su kama sana'ar noma rani da damina domin ci gaba da kasancewa cikin zamantakewa mai albarka da Kuma amsa Kiran gwamnatin tarayya na wadata kasa da abinci.
Wannan kiran ya fito ne daga wani matashin manomi, Ali Adamu Kunnawa (Wanda akafi sani da Ali Branco) dake yankin Karamar hukumar Dawakin Tofa a yayin da wakilinmu ya ziyarci katafariyar gonar da yake noman rani, inda ya bayyana cewa matasa sune ginshiki ci gaban kowace kasa, don haka yana dakyau su kasance masu abin yi ta yadda za su dogara da kansu.
Ya ce sana'ar noma tana da albarka sannan akwai samar da aiyukan yi da kawar da hankalin mutane daga tafiya birane neman aiyukan Yi daga yankunan karkara, don haka yana da kyau kowa ya tashi tsaye neman arziki da dogaro dakai ta yadda zamantakewa za ta ci gaba da yin kyau.
Malam Ali Adamu Branco ya bayyana cewa yana noma masara da gero da maiwa da wake da dawa da Kuma gyada idan damina ta sauka, sannan yana noma albasa da tumatur da alayyahu da tattasai da sauran kayan lambu da rani domin ganin ya kasance cikin dogaro dakai saboda ganin yadda zamani ya juya.
Matashin manomin ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa jagorancin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda kulawa da matasa da take yi wanda a cewar sa, hakan yana taimakawa wajen rage marasa aikin Yi da kawar da aikata laifuka cikin al'uma, sannan ya roki gwamnati da ta samar da tallafi ga matasa manoma ta yadda za su rubanya aiyukan su na noma rani da damina.
A karshe, Ali Adamu Branco ya Yi Kira ga shugaban Karamar hukumar Dawakin Tofa da ta gyara masu Dam din Kunnawa wanda kafin karyewar sa Yana samar da damar yin noman rani ga dumbin al'uma inda ake noma kayan lambu na miliyoyin kudade, tareda fatan cewa wannan sabuwar shekara ta zamo Mai tarin albarka ga al'umar jihar Kano da kuma kasa baki daya





1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here