Yaƙin Iran ne ya janyo wa jam’iyyarmu rashin nasara – Trump
Shugaban Amurka ya ce yaƙinsa da Iran ne ya janyo wa jam’iyyarsa ta Republican gagarumar koma-baya a zaɓen tsakiyar wa’adi na ƙasar.
Kawo yanzu dai jam’iyyar ta rasa rinjaye a duka majalisun dokokin ƙasar biyu.
Yayin wata hira da kafar yaɗa labarai ta Fox News, Shugaba Trump ya ce yaƙin ya haddasa tashin farashin Gas a Amurka wanda kuma shi ne ya janyo wa Repblican baƙin jini.
Ku kuma karanta: Gwamnan Katsina Ya je Ta’aziyya Ga iyalan Marigayi Sheikh Masussuka
”Mutane suna ji a jikinsu saboda suna sayen gas da tsada”, in ji shi.
Shugaban na Amurka ya kuma ce dole Amurka ta yi wani abu kan Iran
“Ba za mu bari su mallaki makamin nukiliya ba,” a cewar Shugaba Trump.


