BIZ Sister Kano Ta Gudanar da Taron Ƙarfafa Mata Kan Harkokin Kasuwanci
Daga Shafaatu Dauda Kano
Ƙungiyar Matasan Mata ‘Yan Kasuwa reshen Jihar Kano, BIZ Sister Kano, ta gudanar da wani taron ƙara wa juna sani da ƙarfafa gwiwa kan harkokin kasuwanci.
Taron ya mayar da hankali ne wajen bunƙasa ilimin kasuwanci, musayar dabaru da ƙwarewa, tare da ƙarfafa wa mata gwiwar ci gaba da gudanar da sana’o’insu domin samun ci gaba da dogaro da kai.

Mahalarta taron sun samu damar tattauna ƙalubalen da suke fuskanta a harkokin kasuwanci, da kuma hanyoyin da za su taimaka wajen bunƙasa sana’o’insu da faɗaɗa kasuwancinsu.
Ku kuma karanta: Al’ummar Unguwar Kurna da ke Kano Sun Koka Kan Rashin Hanya
A nata jawabin, Shugabar Ƙungiyar, Shema’u Khabeer (Sheema Collection), ta yi kira ga ‘yan kasuwa da su kasance masu haƙuri da juriya wajen gudanar da harkokin kasuwancinsu, tana mai cewa nasara a kasuwanci na buƙatar jajircewa, haƙuri da dagewa.
Ta kuma ƙarfafa wa mata gwiwar kada su karaya sakamakon ƙalubalen da suke fuskanta, sai dai su ci gaba da neman ilimi, sabbin dabaru da haɗin kai domin bunƙasa kasuwancinsu.


