Al’ummar Unguwar Kurna da ke Kano Sun Koka Kan Rashin Hanya
Daga Shafaatu Dauda
Mazauna yankin Anguwar Kurna Karshen Kwalta zuwa Kurna Tudu dake Karamar Hukumar Ungogo ta jihar Kano sun koka kan rashin kyakkyawar hanyar mota, inda suka ce matsalar ta jima tana addabarsu ba tare da gwamnati ta dauki matakin magance ta ba.
Mazauna yankin sun shaidawa wakiliyar Neptune Prime cewa sun kwashe shekaru suna kai koken rashin hanyar ga hukumomin gwamnati, amma har zuwa yanzu babu wani ingantaccen mataki da aka dauka na duba halin da suke ciki ko sauraron kokensu.
Sun ce abin da ya fi damunsu shi ne, a duk lokacin da zabe ya matso, sai wasu ‘yan siyasa su rika ziyartar yankin tare da yi musu alkawura na gyara hanya, amma bayan zabe komai ya koma yadda yake.
Ku kuma karanta: Yadda aka yi bikin al’adu na ABUSRC a ABU Zariya
Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa duk lokacin da aka samu ruwan sama, suna shiga cikin mawuyacin hali, domin hanyar na cika da ruwa da laka, lamarin da ke sanya zirga-zirga cikin wahala tare da jefa jama’a cikin hadari.
“Da zarar an yi ruwa, muna shiga cikin rudani. Ba mu da hanyar wucewa cikin kwanciyar hankali, musamman ga masu zuwa aiki, makaranta da sauran harkokin yau da kullum,” in ji wani mazaunin yankin.
A yayin da wakiliyar Neptune Prime ke daukar wannan rahoto, wasu fusatattun matasa daga yankin sun bayyana takaicinsu kan yadda matsalar ta dade ba tare da an magance ta ba.
Matasan sun yi kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar matakin gyara hanyar domin rage wahalhalun da mazauna yankin ke fuskanta, musamman a lokacin damina.
A cewarsu, ya kamata gwamnati ta mayar da hankali kan gyaran titunan cikin gari da ke matukar bukatar gyara, maimakon mayar da hankali kan titunan da a halin yanzu ba sa bukatar wani gagarumin gyara.
Sun ce duk da yawan koke-kokensu, har yanzu ba a dauki matakin da ya dace na kawo musu dauki ba, lamarin da suka ce ke kara jefa al’ummar yankin cikin wahala.
Sun kuma ce sun dade suna jiran ganin sauyi, inda suka bayyana cewa, “an dade ana ruwa, kasa tana shanyewa,” amma har yanzu ba a samu wani gagarumin sauyi ba.


