Ƙungiyar ‘Yan Jarida a Jihar Yobe ta Zaɓi Sabbin Shugabanni, Mamudo Ya Zama Sabon Shugaban Ƙungiyar
Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Yobe, ta gudanar da zaɓen sabbin shugabanninta da za su jagoranci ƙungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa, inda Alhaji Alhassan Sule Mamudo ya samu nasarar zama sabon shugaban ƙungiyar bayan samun gagarumar nasara a zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar 28/11/2026.
Zaɓen, wanda aka gudanar a Cibiyar ’Yan Jarida ta NUJ da ke Damaturu, ya bai wa Alhassan Sule Mamudo nasarar samun ƙuri’u 199, inda ya doke sauran ’yan takararsa, Suleiman Gambo Bakaro, wanda ya samu ƙuri’u takwas, da Usman Mohammed Nasoro, wanda ya samu ƙuri’u 14.
A zaɓen kujerar mataimakin shugaban ƙungiyar kuwa, Usman Ibrahim Geidam na Sahel Treasure Chapel ne ya yi nasara da ƙuri’u 181, inda ya kayar da abokin takararsa, Usman Nasidi na Yobe State House of Assembly Chapel, wanda ya samu ƙuri’u 33.
Ku Kuma Karanta: Zargin cin zarafi: Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura
A yayin da aka gudanar da zaɓen sauran muƙamai biyar na shugabancin ƙungiyar ta hanyar maslaha, inda dukkan ’yan takarar da aka amince da su suka samu damar fitowa ba tare da hamayya ba.
Waɗanda suka samu waɗannan muƙamai sun haɗa da Abdulaziz Mohammed Shehu na YTV Chapel a matsayin Sakatare; Ahmed Isah Abba na Correspondents Chapel a matsayin Mataimakin Sakatare; Mohammed Dala Lawan na Sunshine FM Chapel a matsayin Mai Binciken Kuɗi (Auditor); Yusuf Bukar Biriri na YBC Chapel a matsayin Ma’aji; sai Aliyu Mohammed Babi na NTA Chapel a matsayin Sakataren Kuɗi.


A jawabinsa na godiya bayan samun nasarar zaɓensa, sabon shugaban ƙungiyar, Alhaji Alhassan Sule Mamudo, ya bayyana matuƙar godiyarsa ga mambobin ƙungiyar bisa irin gagarumar amincewar da suka nuna masa ta hanyar zaɓensa.
Ya yi alƙawarin gudanar da shugabanci bisa gaskiya, riƙon amana da adalci, tare da tabbatar da haɗin kai, ƙwarewa a aikin jarida da kuma inganta jin daɗin walwalar ’yan jarida a faɗin jihar Yobe.

Haka kuma, Mamudo ya buƙaci dukkan mambobin ƙungiyar da su ba sabon shugabancin goyon baya da haɗin kai, yana mai jaddada cewa samun ci gaba mai ma’ana a cikin ƙungiyar na buƙatar haɗin gwiwa, sadaukarwa da kuma fahimtar nauyin da ke kan kowa.
Zaɓen ya gudana ne ƙarƙashin kulawar hedikwatar ƙasa ta NUJ, inda Sakataren Shiyyar Arewa maso Gabas, Abubakar Waziri, ya wakilci shugabancin ƙungiyar na ƙasa.
An kammala zaɓen ne da miƙa takardun shaidar nasara ga sabbin shugabannin da aka zaɓa.


