Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

Adres güncellemeleriyle sorunsuz bağlantı sağlayan bettilt önemlidir.

Bahis sektöründe kullanıcıların %61’i canlı bahisleri tercih ederken, bettilt giriş bu segmentte yüksek oranları ve hızlı işlem avantajıyla öne çıkmaktadır.

Futbol, basketbol ve daha pek çok spor dalında kupon yapmak için bahsegel bölümü tercih ediliyor.

Mobil deneyimini geliştiren bettilt sistemi oldukça popüler.

OECD 2024 raporuna göre, Avrupa’daki lisanssız bahis sitelerinin oranı %35’tir; bu, bettilt giriş gibi lisanslı sitelerin önemini artırır.

bahsegel bahsegel giriş bahsegel bettilt bahsegel giriş bahsegel giriş bahsegel giriş bahsegel giriş paribahis

Dijital ortamda oyun keyfini artıran https://paribahis-resmi.ink/ kategorileri öne çıkıyor.

bahsegel güncel giriş bahsegel güncel giriş bahsegel güncel giriş
HomeLabariNNPP ta kai...

NNPP ta kai ƙarar ƴan majalisa 45 saboda sauya sheƙa daga jam’iyyar

NNPP ta kai ƙarar ƴan majalisa 45 saboda sauya sheƙa daga jam’iyyar

Jam’iyyar NNPP ta shigar da ƙara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, tana ƙalubalantar sauya sheƙar ’yan majalisa 45 da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar a zaɓen 2023.

Ƙarar, wadda ta shafi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ’yan majalisar, ta ƙunshi mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano 28, ’yan Majalisar Wakilai 18 da Sanatoci biyu, kamar yadda jam’iyyar ta bayyana a wata takarda da ta aika wa INEC.

NNPP ta yi zargin cewa ’yan majalisar sun koma wasu jam’iyyu ba tare da kammala matakan murabus daga cikinta ba, duk da cewa har yanzu suna riƙe da kujerun da suka samu a ƙarƙashin inuwarta.

Jam’iyyar ta kuma nuna damuwa kan yadda wasu daga cikin ’yan majalisar suka bayyana a jerin sunayen ’yan takarar wasu jam’iyyu na zaɓen 2027 da INEC ta fitar.

A cikin ƙarar, NNPP ta nemi kotu ta fassara tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, musamman sassan 68 da 109, waɗanda suka tanadi yanayin da ɗan majalisa zai iya rasa kujerarsa bayan sauya sheƙa.

Ta kuma buƙaci a ɗauki matakan da suka dace, ciki har da ayyana kujerun waɗanda sauya sheƙarsu ta saɓa wa doka a matsayin waɗanda suka zama babu kowa, tare da gudanar da zaɓen cike gurbi.

NNPP ta ce ba ta haɗe da wata jam’iyya ba, kuma tana nan a matsayin jam’iyyar siyasa mai rijista, don haka ba ta ga dalilin da zai ba ’yan majalisar damar sauya sheƙa ba tare da rasa kujerunsu ba.

A ranar 19 ga Oktoba ne jam’iyyar ta aika wa INEC wasiƙa kan lamarin, inda ta nemi hukumar ta gudanar da bincike.

Wanda ya kafa NNPP kuma Shugaban Kwamitin Amintattunta, Dakta Boniface Aniebonam, ya kuma yi gargaɗin cewa jam’iyyar ba za ta amince da duk wani yunƙuri na mayar da ranar murabus ɗin ’yan majalisar baya domin halatta sauya sheƙarsu ba.

Ya ce yin hakan zai zama karya doka, tare da kira ga duk masu neman takardun murabus na baya da su guji irin wannan mataki.

Ƙarar na neman a fayyace matsayin dokar ƙasa kan sauya sheƙar ’yan majalisa da kuma alhakin INEC wajen tabbatar da bin dokokin zaɓe gabanin zaɓen 2027.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

Yaƙin Iran ne ya janyo wa jam’iyyarmu rashin nasara – Trump

Yaƙin Iran ne ya janyo wa jam'iyyarmu rashin nasara - Trump Shugaban Amurka ya ce yaƙinsa da Iran ne ya janyo wa jam'iyyarsa ta Republican gagarumar koma-baya a zaɓen tsakiyar wa'adi na ƙasar. Kawo yanzu dai jam'iyyar ta rasa rinjaye a...

‘Yan bindiga sun sace ɗaliban Islamiyya 14 da malamansu a Neja

'Yan bindiga sun sace ɗaliban Islamiyya 14 da malamansu a Neja Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban makarantar Islamiyya 14 tare da malaminsu a ƙauyen Tungan-Bako da ke gundumar Pandogari, ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja. An sace mutanen...

Wane ne Sheikh Yahaya Masussuka da ‘Yan Bindiga Suka Kashe?

Wane ne Sheikh Yahaya Masussuka da 'Yan Bindiga Suka Kashe? Sheikh Yahya Masussuka, fitaccen malamin addinin Musulunci ne daga jihar Katsina, ya shafe sama da shekaru 30 yana wa'azi, tun yana ɗan shekara 13. An haifi Sheikh Yahya Masussuka a ranar...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.