Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

Adres güncellemeleriyle sorunsuz bağlantı sağlayan bettilt önemlidir.

Dijital ortamda eğlencenin en güvenilir adresi bettilt oluyor.

HomeLabariBIZ Sister Kano...

BIZ Sister Kano Ta Gudanar da Taron Ƙarfafa Mata Kan Harkokin Kasuwanci

BIZ Sister Kano Ta Gudanar da Taron Ƙarfafa Mata Kan Harkokin Kasuwanci

Daga Shafaatu Dauda Kano

Ƙungiyar Matasan Mata ‘Yan Kasuwa reshen Jihar Kano, BIZ Sister Kano, ta gudanar da wani taron ƙara wa juna sani da ƙarfafa gwiwa kan harkokin kasuwanci.

Taron ya mayar da hankali ne wajen bunƙasa ilimin kasuwanci, musayar dabaru da ƙwarewa, tare da ƙarfafa wa mata gwiwar ci gaba da gudanar da sana’o’insu domin samun ci gaba da dogaro da kai.

Mahalarta taron sun samu damar tattauna ƙalubalen da suke fuskanta a harkokin kasuwanci, da kuma hanyoyin da za su taimaka wajen bunƙasa sana’o’insu da faɗaɗa kasuwancinsu.

Ku kuma karanta: Al’ummar Unguwar Kurna da ke Kano Sun Koka Kan Rashin Hanya

A nata jawabin, Shugabar Ƙungiyar, Shema’u Khabeer (Sheema Collection), ta yi kira ga ‘yan kasuwa da su kasance masu haƙuri da juriya wajen gudanar da harkokin kasuwancinsu, tana mai cewa nasara a kasuwanci na buƙatar jajircewa, haƙuri da dagewa.

Ta kuma ƙarfafa wa mata gwiwar kada su karaya sakamakon ƙalubalen da suke fuskanta, sai dai su ci gaba da neman ilimi, sabbin dabaru da haɗin kai domin bunƙasa kasuwancinsu.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

Al’ummar Unguwar Kurna da ke Kano Sun Koka Kan Rashin Hanya

Al’ummar Unguwar Kurna da ke Kano Sun Koka Kan Rashin Hanya Daga Shafaatu Dauda Mazauna yankin Anguwar Kurna Karshen Kwalta zuwa Kurna Tudu dake Karamar Hukumar Ungogo ta jihar Kano sun koka kan rashin kyakkyawar hanyar mota, inda suka ce matsalar...

Yadda aka yi bikin al’adu na ABUSRC a ABU Zariya

Yadda aka yi bikin al’adu na ABUSRC a ABU Zariya Daga Idris Umar, Zariya Majalisar Wakilan Ɗalibai ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABUSRC) ta fara bikin al’adunta, inda aka fara da gasar girke-girke tsakanin ɗalibai daga jihohi da kabilu daban-daban. An gudanar da...

Cikin Ruwan Sama, Islamiyyoyi sama da 700 ne suka fito zagayen Mauludin Annabi (SAWW) a Potiskum

Cikin Ruwan Sama, Islamiyyoyi sama da 700 ne suka fito zagayen Mauludin Annabi Muhammad (SAWW) a Potiskum Cikin mamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, ɗaruruwan al'ummar musulmi haɗe da makarantun Islamiyyoyi sama da 700 ne suka fito zagayen Mauludin...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.