Daga; Rabo Haladu.
DAN takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana sunan Alhaji Kabir Ibrahim Masari a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na shekarar 2023.
Tinubu ne ya mika sunan Kabir Masari ne a matsayin wanda zai tsaya gabanin wa’adin da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ba jam’iyyu na su mika sunayen ‘yan takararsu a zaben 2023.
Wasu majiyoyi daga bangaren Tinubu da Masari sun tabbatar da haka a yammacin ranar Alhamis.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC ya fito ne daga kauyen Masari da ke karamar hukumar Kafur a jihar Katsina kuma dan uwan Rt. Hon. Aminu Bello Masari, Gwamnan Katsina ne.
Mataimaki na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya taba zama sakataren jindadi da walwala na kasa a jam’iyyar APC a lokacin Kwamared Adams Oshiomhole yana matsayin Shugaban Jam’iyyar na kasa.