Ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a gidan mutuwa

0
21
Ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a gidan mutuwa

Ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a gidan mutuwa

Wani ɗan ƙunar baƙin wake ya yi basaja, tare da tayar da bam a gidan mutuwa a Dalori da ke Jihar Borno.

Harin ya yi sanadin mutuwar mutum biyu tare da jikkata mutum ɗaya.

Wani jami’in tsaro ya ce: “Ɗan ƙunar baƙin waken ya yi basaja a matsayin wanda ya zo yin ta’aziyya, kafin daga bisani ya tayar da bam ɗin.”

Jami’an tsaro sun garzaya zuwa wajen bayan samun labarin fashewar bam ɗin.

A cewar wani jami’in tsaro, an fara gudanar da bincike don gano asalin wanda ya kai harin da kuma yadda ya kai harin.
Majiyoyi sun ce an garzaya da wanda ya jikkata zuwa asibiti domin samun kulawa.

Jami’an tsaro sun ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin domin hana sake aukuwar irin wannan hari.

KU KUMA KARANTA: Harin ƙunar baƙin wake ya kashe mutane 6 a Borno – ‘Yansanda

“Dole ne mu kasance masu lura a kowane lokaci, saboda har yanzu akwai barazanar hare-hare daga ’yan ta’adda.

“Za mu ci gaba da yin aiki tuƙuru don kare al’umma,” in ji wani jami’in tsaro.

Hare-haren sun sanya fargaba a zukatun mazauna yankin, inda mutane ke kiran gwamnati da jami’an tsaro su ƙara tsaurara matakan tsaro a wuraren da suka fi fuskantar barazanar ta’addanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here