Connect with us

Labarai

Ƴan sandan Najeriya sun kama waɗanda ake zargi da satar mutane a titin Abuja-Kaduna

Published

on

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce ta kama mutanen da ake zargin su da kitsa tare da yawan sace mutane a kan Titin Abuja zuwa Kaduna.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Kaduna yayin holen mutanen a hedikwatar rundunar ta Jihar Kaduna, jami’in hulɗa da jama’a Muyiwa Adejobi ya ce cikin wadanda aka kama har da waɗanda ake zargi da kashe ɗaliban Jami’ar Greenfield ta Kadunan.

Ya ce daga cikinsu har da wani “riƙaƙƙen ɗan ta’adda” Ibrahim Abdullahi wanda aka fi sani da Mande, da ake zargin shi ne ya kitsa tare da jan ragamar sace ɗaliban Jami’ar Greenfiled da kashe wasun su, da kuma jagorantar yawan satar mutane da ake yi a kan Titin Abuja-Kaduna.

Mista Muyiwa ya ce an kama Mande ne bayan samun wasu sahihan bayanai da aka yi a Rido Junction na ƙaramar hukumar Chikun a kan hanyar Abuja zuwa Kadunan.

KU KUMA KARANTA: Najeriya ta samu tallafin dala biliyan 1.3 Don ƙarasa hanyar jirgin ƙasa daga Kano zuwa Nijar

Jami’in ya ce mutumin ya amsa cewa shi ne shugaban wani gungu da ke tayar da hankalin mutane a kan Titin Abuja-Kaduna, kuma an sanya shi a jerin riƙaƙƙun ƴan bindiga irin su Dogo Gide da Bello Turji.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an kama bindigogi kirar AK-47 guda 48 a yayin da aka kama Mandi kuma ana ci gaba da kokarin gano masu ɗaukar nauyinsa da kuma masu ba shi makamai.

A ranar 20 ga watan Afrilun 2021 ne aka sace daliban jami’ar Greenfield 20 da malamansu biyu, kwana uku bayan nan kuma aka gano gawar takwas daga ciki, yayin da aka saki sauran mutum 14 din ranar 29 ga watan Mayun 2021, bayan sun shafe wata guda a hannun ‘yan bindigar.

Kazalika kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa jami’an tsaron sun kuma kama wani riƙaƙƙen shugaban ƴan bindigar wanda ya kitsa harin da aka kai Cocin Saint Raphael a Fadan Kamantan a watan Satumban 2023.

Rundunar ƴan sandan ta kuma bayyana yadda ta kama wani mutum Shedrack John da ake zarginsa da taimaka wa masu satar mutane da abin da ya shafi kula da lafiyarsu a cikin daji.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya tabbatar da cewa, Sufeto Janar Kayode Egbetokun yana ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da doka da oda, da tabbatar da tsaro da tsaron dukkan ‘yan kasa, da kuma yaki da miyagun ayyuka a faɗin ƙasar.

“Wadannan nasarorin da aka samu a hanyar Abuja zuwa Kaduna a baya-bayan nan na nuna kishin rundunar wajen cika aikinmu na kare rayuka da dukiyoyi. Za a gudanar da irin wannan aikin na musamman a sauran manyan titunan kasar ta hanyar kafa runduna ta musamman da za ta saka ido,” in ji shi.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like