Ƙungiyar ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki a jami’ar Maitama Sule

0
186

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, reshen Jami’ar Yusuf Maitama da ke Kano, ta koka kan rikicin da ke shirin kunno kai, idan har gwamnatin jihar ta gaza magance buƙatunta.

Ƙungiyar ta yi zargin cewa gwamnatin jihar ta shafe watanni tana yin watsi da buƙatunsu.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da shugaban reshen da kuma sakataren ƙungiyar Mansur Sa’ id da Yusuf Gwarzo suka sanya wa hannu a ranar Alhamis a Kano.

KU KUMA KARANTA:Zulum ya buƙaci Sojoji su samar da sansani a dajin Sambisa

Ya ce buƙatunsu guda uku ne waɗanda suka haɗa da inganta yanayin aiki ga mambobinsu.

Sauran kuma sun haɗa da bunƙasawa da kuma hanzarta samar da ci gaban jami’ar ta hanyar bayar da kuɗaɗen aiki mai ɗorewa, ƙarfafawa da kare ikon cin gashin kai na jami’a da ‘yancin ilimi.

Ƙungiyar ta ce ba ta so ta bayyana yanayin a fili ba amma ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na ganin ta biya musu buƙatunsu ya ci tura.

Leave a Reply