Ƙo kasan amfanin taura a jikin ɗan Adam?

0
460

Wannan Bishiya mai suna Taura tana da zaƙi da ɗan bauri kaɗan wanda baurin nata ba ya hana a ci, zaƙin nata kuma ba shi da illa.
Tana maganin cutukan daji wato ‘cancer’ a turance.

Macen da take samun ciki yana yawan ɓarewa wato ‘miscarriage’ sai ta nemi wannan tauran ta rinƙa ci akai-akai.

Taura tana maganin tarin asma, sai a jiƙa ta a cikin ruwan zafi a rinƙa sha kullum da safe. Tana maganin zafin naƙuda, sannan tana maganin kumburin ciki. Taura tana ƙara wa hanta da ƙoda lafiya.

Masu fama da cutar Sikla, wato ‘sickle cells’ su rinƙa shan shayin Taura. Za su samu sauƙin wannan ciwon sosai.

KU KUMA KARANTA: Anfanin ayaba 12 da ya haɗar da kiyaye lafiyar ƙoda, anfani ga mata masu juna biyu, da taimakawa ƙwaƙwalwar ɗalibai

Macen da naƙuda ta yiwa nauyi a nemi garin Taura a yi shayi a ba ta ta sha Insha Allahu cikin ƙanƙanin lokaci za ta haihu. Macen da ta haihu ya zamo ba ta da ruwan Nono ta rinƙa cin Taura. Mata masu son samun cikakkiyar sha’awa su rinƙa cin Taura.

Mai fama da yawan mantuwa ya rinƙa cin taura zai ga abun mamaki. Mai fama da ƙarancin bacci, ya nemi garin taura ya rinƙa jiƙawa a ruwa yana sha zai ga biyan buƙata.
Mai fama da hawan jini ya maida taura abincin shi a kai-akai zai yi mamaki.

Mai ciwon zuciya da jin ƙuna a kan murfin zuciya ya rinƙa shan shayin taura. Mai fama da tsananin damuwa na ƙwaƙwalwa waton ‘depression’ ya rinƙa shan shayin taura.

Namijin da yake da ƙarancin ruwan maniyyi wanda ba su kai mil 4 zuwa 5 ba, ya rinƙa cin taura. Taura tana sanya cin abinci (natural appetizer).

Leave a Reply