Zulum ya bada sanarwar tallafin naira biliyan ɗaya ga waɗanda gobarar kasuwa ta shafa a Maiduguri

2
404

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya sanar da bayar da agajin gaggawa na naira biliyan 1 ga waɗanda gobarar kasuwar Monday Market ta shafa a Maiduguri, jihar Borno.

Gwamnan ya ziyarci kasuwar da safiyar lahadi bayan da gobara ta ƙona kantuna da dama. Ya ce kuɗaɗen za su bayar da tallafin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa, har sai an tantance lamarin.

Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Zulum ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, ya kuma haɗa da sojoji masu ɗauke da makamai domin tabbatar da tsaro a yankin domin daƙile taɓarɓarewar doka da oda.

Sanarwar ta ce, “Mun tashi ne a yau da wani mummunan bala’in tashin gobara a kasuwar litinin da ke Maiduguri. Wannan abin takaici ne matuka, amma mun yi imani da cewa Allah ne ya kaddara. Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun. Na ji zafi sosai da wannan lamarin kuma na san yadda yake da zafi ga kowa ya yi aiki tuƙuru tsawon shekaru don gina kasuwancinsa amma ya ƙare ya rasa wannan jarin cikin daƙiƙa.

KU KUMA KARANTA: An Yi Gobara A Wani Sashen Gidan Sheikh Gumi A Kaduna

“Ina jin raɗaɗin duk wanda wannan lamari ya shafa. Ina jajanta ma dukkan ku. Ina mai ƙira gareku cikin ladabi da girmamawa da ku nutsu da hakuri. Nasan yadda kuke ji kuma insha Allahu tuni gwamnatin jihar Borno ta fara daukar wadannan matakai domin gyara lamarin.

“Na amince da sakin Naira biliyan 1 a matsayin agajin gaggawa don tallafa wa wadanda bala’in ya rutsa da su cikin gaggawa domin mun san cewa wasu daga cikinsu na iya samun wahalar rayuwa nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.

Mutane da yawa sun dogara ga kasuwancin yau da kullun don biyan bukatun kansu. “Muna kafa kwamitin tantancewa wanda zai kunshi mutane masu mutunci daga cikin al’ummarmu da suka hada da wakilan wadanda abin ya shafa, domin mu gaggauta tantance irin barnar da aka yi, da kuma daukar cikakken jerin wadanda abin ya shafa da kuma asarar da suka yi.

Zan kuma yi taro da shugabannin kasuwar da wakilan waɗanda abin ya shafa. “Zan ga shugaban ƙasa kuma in nemi taimakon shi kan yadda zan samu tallafi ga waɗanda abin ya shafa.

“Za kuma mu kai ga sauran cibiyoyin jin kai don neman taimako. In sha Allahu zamu ɗauki kwararan matakai na hana sake afkuwar wannan bala’in gobara da ya faru a shekarun baya. “Ina so in yi kira ga kowa da kowa domin ya samu nutsuwa, na san yadda kuke ji.

Ina jin zafin, kuma za mu tallafa muku ta duk hanyar da za mu iya, insha Allahu. “A halin yanzu, ina kira gare mu da kada mu sanya siyasa a wannan lamari mara dadi. Na gane cewa lamarin yana faruwa a lokacin siyasa, amma duk mun san kasuwar litinin ta fuskanci bala’in gobara a lokutan baya kuma wannan abin bakin ciki ne.

“Dole ne mu nemo hanyoyin da za mu tabbatar da cewa wannan bala’in gobara bai sake faruwa ba kuma za mu yi aiki tare don tabbatar da hakan.”

2 COMMENTS

Leave a Reply