Zanga-zanga: Mata da matasa sun yi biris da umarnin gwamnan Kaduna

0
76
Zanga-zanga: Mata da matasa sun yi biris da umarnin gwamnan Kaduna

Zanga-zanga: Mata da matasa sun yi biris da umarnin gwamnan Kaduna

Sai dai kuma duk da ya ke an yi zanga-zangar ta ranar farko aka kammala lami lafiya a Zariya, a cikin garin Kaduna zanga-zangar ta juye ya zuwa lalata kayan gwamnati da wasu jami’an tsaro.

Duk da alwashin da Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya yi na cewa ba za a yi zanga-zanga a jihar ba, mata da matasa sun cika manyan titunan biranen Kaduna da Zariya domin bin takwarorinsu a sauran sassan Najeriya wajen bayyana damuwar su kan matsalar tsaro da tsadar rayuwa.

Sai dai kuma duk da ya ke an yi zanga-zangar ta ranar farko aka kammala lami lafiya a Zariya, a cikin garin Kaduna zanga-zangar ta juye ya zuwa lalata kayan gwamnati da wasu jami’an tsaro.

Mata da matasa sun fito cikin lumana da haɗin kai suka fara zanga-zangar a cikin garin Kaduna har zuwa wani lokaci, kafin daga bisani aka sami wasu matasan da suka fara jefe-jefe a ƙofar gidan gwamnatin jihar, wanda hakan ya sa jami’an ‘yan-sanda suka fara harba barkonon tsohuwa.

KU KUMA KARANTA;Gwamnatin Kaduna ta nisanta kanta akan bidiyon dukan Ɗan-Balki kwamanda

Bayan tarwatsa masu zanga-zangar daga ƙofar fadar gwamnatin ne sai su kuma matasan su ka fara aukawa ofisoshin wasu hukumomin gwamnatin jihar Kaduna da ke kusa, kamar dai yadda mai-magana da yawun rundunar ‘yan-sandan jihar ta Kaduna ASP Mansur Hassan ya shaidawa Muryar Amurka.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar da aka fara cikin lumana sun nuna damuwa kan yadda ta juye zuwa tashin hankali daga baya.

Sai dai kuma a lardin Zazzau an yi zanga-zangar lami lafiya, inda har sai da mai martaba sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya fito, ya karɓi koken masu zanga-zangar kuma ya yi musu jawabi.

Kwanaki goma ne masu zanga-zangar ƙuncin rayuwa suka ɗiba na kasancewa akan tituna, to sai dai kuma ganin yadda zanga-zangar ta juye zuwa barna a wasu yankunan, ya sa wasu sun fara shakkar yiwuwar kwashe kwanakin goma ana zanga-zangar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here