Zanga-Zanga: BUK ta dakatar da koyarwa zuwa wani lokaci

0
70
Zanga-Zanga: BUK ta dakatar da koyarwa zuwa wani lokaci

Zanga-Zanga: BUK ta dakatar da koyarwa zuwa wani lokaci

Daga Ali Sanni

Hukumar Gudanarwar Jami’ar Bayero ta Kano, ta sanar da dakatar da ɗaukar darusa zuwa wani lokaci, sakamakon zanga-zangar adawa da yunwa da ake ci gaba da yi a faɗin ƙasa.

Wata sanarwa da Jami’ar ta fitar ranar Litinin, ta ce ta ɗauki matakin ne bayan zama datayi da duba batun zanga-zangar da ake yi a jahar.

“Mun damu da lafiyar ɗaliban mu da tsaron su    da kuma dukiyoyinsu, shi ya sa muka ɗauki wannan matakin.

KU KUMA KARANTA: Zanga-Zanga: An sa dokar hana fita a Kaduna da Zariya

“Muna kira ga ɗaliban da ma’aikatanmu da su ci gaba da kula da irin zirga-zirgar da za su yi a wajen Jami’a domin kaucewa shiga hatsari.”

Jami’ar ta kuma shawarci ɗaliban da ke zaune a cikin makarantar da su kwantar da hankalinsu, sannan su kasance masu bin doka da oda.

Kazalika, Jami’ar ta bayar da tabbacin komawa ɗaukar darusa da zarar al’amura sun daidaita a jihar.

Leave a Reply