Zan yi adalci ga kowa, alƙawarin Tinubu ga ‘yan Najeriya

1
460

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta yi adalci idan aka zaɓe shi.

Tinubu, wanda ya yi magana da harshen yarbanci, ya yi wannan alkawarin ne a wani taro da aka yi da shugabannin musulmi daga kudu maso Yamma a, a ranar Lahadi, a garin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Tinubu, Tunde Rahman, ya fitar a Abuja.

Taron dai ya ci gaba da tattaunawa da ƙungiyoyin addinai da shugabannin addinai a ƙasar domin bayyana shirinsa na sake farfado da tattalin arzikin ƙasa domin amfanin ‘yan Najeriya baki ɗaya.

A yayin da yake bayyana zaɓen 2023 a matsayin ‘muhimmin haɗuwar Najeriya da sama mata makoma, Tinubu ya buƙaci malaman addinin musulunci su wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaɓen ‘yan takarar da aka yi wa jarrabawa, tare da kyawawan ayyukan gwamnati da suka yi aka gani.

Ɗan takarar jam’iyyar APC ya kuma yaba wa malaman bisa ci gaba da addu’o’in da suke yi, inda ya ce ya kamata su cigaba da bai wa mabiyansu kwarin gwiwa ta hanyar ƙarfafasa da cewa kada su guji ‘faɗin karya da ƙage-ƙage na waɗanda ba su da wani abin yi.

Ya ce: “Alƙawarin da na yi na tabbatar da gaskiya da adalci ya yi daidai da ƙa’idojin addinin Musulunci.

“Wannan kakar zaɓe ta kasance tattare tarin gaskiya da karya. Ina son zaɓen ya kasance a bisa gaskiya da gaskiya.

“A duba mai aikin da ɗan takara yayi, kuma menene manufofinsa. Ina rokon ku da ku yi kira ga mabiyanku da su fito su kaɗa ƙuri’a su, su yi hakan cikin hikima. Ku zaɓi dan takarar da ke da hangen nesa don samar da zaman lafiya da wadata a Najeriya, inda juriya da jin kai suka tauye hakkinmu na tsarin mulki da na shari’a.”

“Shugaba a jam’iyya irin namu, an umurce shi ya zama shugaban kowa. Idan aka zabe ni, zan yi mulki bisa gaskiya da dimokraɗiyya bisa tsarin mulkin kasarmu.” inji Asiwaju.

KU KUMA KARANTA:Dalilin da ya sa na wakilta su El-Rufai su amsa min tambayoyi a Chatham House – Tinubu

A yayin da yake bayar da misali da kyakkyawan shugabancin da ya yi a matsayinsa na gwamnan jihar Legas, Tinubu ya yi alkawarin yin amfani da wannan gogewar wajen jagorantar Najeriya cikin ruhin ƙirƙire-ƙirƙire da hangen nesa mai inganci don ɗaukaka al’umma da sabunta fata ga ‘yan Najeriya.

Dangane da batun tsaro, ya sha alwashin kawo ƙarshen mulkin ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifuka ta hanyar ɗaukar ƙarin ma’aikata da za a horas da su, baya ga samar da ƙarin kayan aikin tsaro da na’urori don yaki da masu aikata laifuka.

“Game da tattalin arziki, muna neman gyara ainihin tsarin tattalin arzikin, ba za mu iya ci gaba da bunƙasa a matsayin tattalin arziƙin ƙasa bisa haƙar albarkatun ƙasa ba.

“Dole ne mu zama masu kuzari, tattalin arziki iri-iri inda masu son yin aiki za su iya samun aiki mai kyau, amma kuma mu zama al’umma mai isasshiyar tausayi don taimakon waɗanda ba za su iya taimakon kansu ba.

“Dole ne mu farfaɗo da masana’antu da ci gaban masana’antu ta yadda za a samar da ayyukan yi tare da samar da kayayyaki da ayyukan da ke inganta rayuwar talakawan ta yau da kullum.

“Muna neman mafi ƙarancin kashi 6 cikin 100 duk shekara ta hanyar gyara manufofinmu na masana’antu, inganta ababen more rayuwa, inganta ɓangaren wutar lantarki da kuma yin garambawul ga kasafin kudi,” in ji Tinubu ga shugabannin Musulmi.

Da yake mayar da martani kan alkawurran da Tinubu ya yi, Jagoran shugabannin musulmin kudu maso Yamma, Shaikh Rasaki Oladejo, ya bayyana cewa taron ya bai wa Tinubu damar tattaunawa da su kan tsare-tsaren da zai yi wa al’ummar ƙasa idan aka zaɓe shi, musamman ta yadda zai mayar da ƙasar nan ƙasa mai girma, ta inda babu wani mutum da za a zalunta.

A cewar babban Jakadan kungiyar Ansar-ur-deen na ƙasa, Sheikh Ahmad Abdulrahman,taron ba wai don kamfen ne ko amincewa da aniya ko wani ɗan takara ba.

Tinubu ya samu rakiyar shugabannin yankin kudu maso yamma tare da mataimakin gwamnan jihar Legas, Dr. Femi Hamzat; ɗan takarar gwamnan Jihar Oyo,na jam’iyar APC,Sanata Teslim Folarin; tsohon kakakin majalisar wakilai, Dimeji Bankole; mataimakiyar darakta Janar na yakin neman zaɓensa, Hadiza Bala Usman; Sanata Fatai Buhari daga Oyo, dayawa masu rike da mukamai da tsofaffin ‘yan majalisar tarayya.

A baya dai ɗan takarar na jam’iyyar APC ya yi mubaya’a da limaman cocin Pentecostal na jihohin Arewa guda 19 da kuma shugabannin kungiyar kiristocin Najeriya, inda ya isar da irin wannan saƙo kamar yadda ya yi wa shugabannin musulmin kudu maso Yamma.

Ya shaida wa shugabannin addinin Kirista cewa idan aka zaɓe shi, zai tafiyar da gwamnati mai dunƙulewa wacce ba zata nuna ƙabilanci ko wariyar addini ba, za kuma ta zamo mai adalci ga dukkan ‘yan Najeriya.

1 COMMENT

Leave a Reply