Daga Shafa’atu DAUDA, Kano
Wani lauya ɗan gwagwamarya mai zaman kansa a jahar Kano, Barista Badamasi Sulaiman Gandu ya rubuta takaddar ƙorafi akan wata sabuwar Waƙar Ado Isah Gwanja mai taken ‘’CASS ko Asosa’’ ga hukuumar Hisbah ta jahar Kano, dan ta ɗauki matakin gaggawa ga me da sabuwar Waƙar.
Barista Badamasi Gandu a cikin takaddar koken tasa, ya ce ‘’hakika Kano babban garin tarihi ne akan addini da tarbiya irinta addinin musulinci, har ya bada misalin cewa a makonnin da suka gabata wani matashi yaje kan Kabari ya yi rashin mutunci kuma nan ta ke rundunar yan sandan jahar Kano suka kama shi don ya girbi abinda ya shuka, wanda Baristan ya jinjina wa jami’an yan sandan bisa wannan namijin ƙokari’’.
‘’Gandu ya kara da cewa sai gashi mun wayi gari da sabuwar waƙa ta fitsara da rashin kunya wadda tana ta yawo a gari, abun mamaki kowa ya yi shiru duk da ba kowa ne ya sami jin labarin Waƙar ba’.
‘’ya ce a matsayi na na ɗan jihar Kano mai kishin addinin musulinci bazan yi shiru ba.’’ inji Gandu, dan haka ne na ke kira ga hukumar Hisbah da ta ɗauki matakin gaggawa akan daƙile wannan musiba cikin gaggawa nan da kwana uku (3).’’
‘’Ƙin ɗaukar wannan mataki a cikin kwana uku (3) zan dau matakin gurfanar da hisbah agaban kotu mai cikkaken iko .’’
KU KUMA KARANTA: Muna Neman Safara da Mr 442 Ruwa a jallo- Afakallahu
‘’Barista Badamasi Gandu ya yi kira ga mai girma gwamnan jahar Kano, kasancewar sa khadimul Islam mai kuma kishin addinin musulinci, akan Gwamnatin jahar Kano ta ɗauki Ado Isah Gwanja kasancewar haziƙin mawaki aiki a hukumar Hisbah ta jahar Kano, a bashi horo ta yadda zai juyar da basirarsa wajen aikin DA’AWA. Kasance war Gwamnan musulmin ƙwarai, kuma mai daraja da kishin addini, zai aminta ya kuma bawa addini gudunmawa, tare da kiran malamai su tallafi wannan kiran nasa.’
A ƙarshe Badamasi ya nuna takaicinsa na yadda hotunan fitsara da rashin mutunci suke yawo a shafukan sada zumunta a faɗin ƙasar nan wadanda sun saɓa da al’adar mutane da kuma addinin su.
Lawyan yayi kira ga ministan sadarwa, Farfesa Sheik Ali Isah Ibrahim Pantami da ya ɗauki matakin daƙile irin waɗannan waƙoƙi da hotuna, tare da kawo tsarin da hotunan za su daina hawa matukar sun saɓa da al’ada da kuma tarbiyar al’umma.