Zama babbar attajira wadda ta danne Dangote, shine burina – Maimuna Wata Yarinya

Jarumar Kannywood, Maimuna Muhammad wacce aka fi sani da wata yarinya, ta ce babban burinta a rayuwa shine ta zama attajirar ‘yar kasuwa. Maimuna wata yarinya ta ce tana burin ganin ta shahara a fannin kasuwanci ta yadda sunanta zai danne na Dangote ya zama duniya ta san da ita. Jarumar ta kuma ce tana burin ganin ta yi aure ta samu zuri’a dayyiba tare da gamawa da duniya lafiya.

Ta ce za ta so duaceniya ta santa a wannan fage na kasuwanci ta yadda zai kai sunanta ya danne na mai kudin Afrika kuma shahararren dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote.

Maimuna wata yarinya ta bayyana hakan ne a yayin wata da hira da tayi da sashin Hausa na BBC a shirin ‘Daga bakin mai ita’. An tambaye ta menene babban burinta a rayuwa nan gaba inda ta ce:

“Ka san shi dan adam yana da buri a rayuwa. Burina shine a duniyarmu ta yanzu da muke cikinta Ubangiji Allah yasa mu gama da duniya lafiya, shine burin mutum na farko. Sannan kuma burin mutum ba zai wuce yayi aure ya samu zuri’a dayyiba ba a rayuwa, toh wannan ma ina da buri. Amman ni burina shine ina so na zama irin attajiran macen nan yar kasuwa.

Wanda irin ace zan zo ma in danne Dangote a suna, sai ace Hajiya Maimuna wata yarinya. Ka ga kowa yana da burinsa amma ni ina so in zama attajirar yar kasuwa wanda duk duniya za ta san da ita.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *