Zaben 2023: Wata Kungiyar PDP Ta Zargi Dan Majalisar Wakilai Samaila Suleiman Da Yin Zagon Kasa

0
456

Dag; USMAN NASIDI, Kaduna.

WASU Matasan Jam’iyyar PDP dake wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa sun zargi dan majalisar wakilai na Tarayya, Samaila Suleiman da taka rawar gani a fagen yiwa Jam’iyyar zagon kasa a zaben 2023.

A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar Isa Dutse ya fitar, ya yi zargin cewa Suleiman ya koma jam’iyyar adawa a jihar ne domin yin zagon kasa ga kokarin ‘ya’yan jam’iyyar masu gaskiya da kishin kasa wajen ganin an samu nasara a zaben 2023.

Dutse ya yi nuni da cewa har yanzu dan majalisar tarayya na wa’adi biyu bai bayyana ficewarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zauren majalisar ba, ya kara da cewa Suleiman na ci gaba da zama a cikin kusoshin jam’iyya mai mulki, wanda matakin da ya dauka ya sabawa ka’idojin majalisar dokokin kasar.

Ta ce “Samaila Suleiman ya tsaya takara kuma ya ci zabe a jam’iyyar APC a 2015 da 2019, jam’iyyar da ya ce ya fadi zabe ya koma jam’iyyar mu.

“Ba mu yi shakkar gaskiyar Suleiman ba, da ya shiga jam’iyyarmu tun kafin a fara harkokin siyasa a 2023.

“A bayyane yake yana da wata manufa ta sirri da kuma mummunar manufa ta shiga jam’iyyarmu a wannan muhimmin lokaci na shirye-shiryen babban zaben 2023.

“Ya dade yana bayar da kudi domin bai wa wakilai da jami’an PDP na Kaduna ta Arewa a kan cin hanci domin ya samu tikitin jam’iyyar a cikin sauki ta hanyar tauye hakkin ‘ya’yan jam’iyyar da suka tsaya tsayin daka da kuma gaskiyar al’amuran jam’iyyar a mazabar dukda kuwa da irin kunfar bakin da jam’iyyar APC mai mulki ta yi jihar.

“Ya shagaltu da bayar da miliyoyin nairori ga manyan jami’an jam’iyyar wadanda a matsayinsu na wakilai za su taka rawar gani wajen ganin ya zama dan takarar jam’iyyar mu a zaben fidda gwani.

“ Sanin al’umma ne ya bayar da Naira miliyan daya ga kowane Shugaban Jam’iyyar PDP na Unguwanni 12, wanda ya kama Naira miliyan 12 domin sayen ra’ayinsu.

“Wani Naira miliyan 70 kuma ana zarginsa da bayar da shi a cikin mako guda ga jiga-jigan jam’iyyar a jihar Kaduna domin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar.

“Kudaden da ya kamata ya yi amfani da su wajen samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar mazabarsa, ana bayar da su ga daidaikun mutane ne domin su yi mubaya’a.

“Irin wannan mutumin ba zai zama alheri ga al’ummarsa wanda zai kawo ci gaba ba idan har ya zama wakilinsu.

“Da farko zai mayar da hankali wajen kwato kudaden da aka kashe wajen kawo jami’an jam’iyyar.

“Irin wannan mutumin ba za a iya dogaro da shi da kuma aminta da ba shi tikitin jam’iyyarmu ba.

“Saboda haka muna kira ga wakilanmu masu daraja da kada su jinginar da makomar ‘ya’yanmu ta hanyar barin kansu a yaudare su da sayen ra’ayinsu wanda daga karshe mutumin zai yi watsi da hadafinmu da burinmu na samar da makoma mai kyau ga ‘ya’yanmu ba,” in ji shi .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here