Zaben 2023: Wata Kungiya Ta Bukaci Sardaunan Badarawa Da Tsayawa Takara A Jam’iyyar PDP

0
377

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

A YAYIN da zaben shekarar 2023 ke gabatowa, wata kungiya mai suna Kaduna Central Progressive Minds (KCPM), ta bukaci Honaranul Usman Ibrahim wanda aka fi sani da Sardaunan Badarawa da ya koma jam’iyyar adawa ta PDP don tsayawa takarar Kujerar Sanata Shiyar Kaduna ta tsakiyar.

Kodinetan kungiyar, Salisu Kanzagi a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, ya bayyana cewa Sardaunan Badarawa zai yi wa talakawa hidima da kuma aiwatar da sha’awar mutanen Kaduna ta tsakiya domin ya zama sanata na gaba a jam’iyyar ta PDP.

Ya kara da cewa Sardaunan Badarawa a matsayin shugaban riko na Kaduna ta Arewa a karkashin jam’iyyar ta PDP, ya samu nasarori da dama da kawo ci gaban karamar hukumar, inda fannin ilimi, jin dadin ma’aikata, ababen more rayuwa, ayyukan jin dadin jama’a aka ba su fifiko tare da samun nasarori masu inganci.

Kanzagi, ya yi nuni da cewa Sardaunan Badarawa ya kasance mai taimakon jama’a da ke bayar da taimako ga mabukata ba tare da la’akari da harkokin siyasa ko addini ba.

“Sardaunan Badarawa ta bangaren gidauniyarsa, ta tallafawa rayuka da dama, musamman mutanen da suka fito daga gidajen marasa galihu, wadanda yawancinsu sun amfana da tallafin karatu, karfafawa, samar da ayyuka a ma’aikatu.“

“Zawarawan da suka yarda su sake yin aure amma ba su da karfin kudi don yin hakan an tanadar musu kayan aikin gida da kuma abubuwan da ake bukata domin aurar da su duk a kokarin rage karuwanci da sauran munanan dabi’u a cikin al’umma.“

“Yan jam’iyyar APC da na PDP duk sun tafi tare da shi don tabbatar da an raba ayyuka ko da yaushe a tsakanin mazauna shiyyar Kaduna ta tsakiya.“

“An sanya fitulun tituna a makabartar Musulmi da Kirista, kananan hukumomin biyu sun amfana da dimbin ayyukan raya al’umma da ya yi wadanda suka yi tasiri ga jama’a.“

“Muna da yakinin cewa Sardaunan Badarawa zai yi wa al’ummarmu hidima a kan dandalin jam’iyyar adawa ta PDP da masu ruwa da tsaki su ka yi ta kiransa da ya shiga don haka za a fara shirye-shiryen da ya dace don ganin ya zama Sanata a matsayin Sanata.“

“Mun kuduri aniyar yin aiki tare da hada hannu da al’umma da kayan masarufi domin tabbatar da aniyar Sanata Sardaunan Badarawa a 2023.“

“Abin da muke so daga gare shi shi ne ya ce ya amince da bukatun mu, ya bar mana sauran mu tabbatar da hakan yayin da muke kara kusantar babban zabe mai zuwa.“

“Sardaunan Badarawa mutum ne mai ban al’ajabi, mai tausayi da kishi da himma wajen yi wa al’umma aiki ta hanyar tabbatar da sun samu abubuwan more rayuwa ta yadda za su yi rayuwa cikin jin dadi da kuma gogayya da takwarorinsu a kasashen da suka ci gaba.”

“Lokaci ya yi da za a ba wa irin wannan mutum abin koyi wata dama wanda yake shi kadara ne da ba kasafai ake samun irinsu a cikinmu ba domin zama a matsayin zababben jami’in gwamnati don ya yi wani abu na daban da zai amfanin jama’armu har izuwa yaranmu da ba a haife su ba,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here