Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.
A YAYIN da mafi akasarin Jam’iyyun siyasa a kasar Najeriya ke kokarin kammala zaben fidda gwani, Shugabar Gidauniyar Kare Hakkin Mata da Kananan Yara a Najeriya, Hajiya Ramatu Tijjani, ta yi kira ga duk masu neman shugabancin kasar nan da su zabi Mata a matsayin mataimakansu ba tare da yin la’akari da yankinta, kabila da addininta ba.
Ramatu ta yi wannan kiran ne a wata tattaunawa da ta yi da ‘yan Jaridu a garin kaduna da nufin jawo hankalin daukacin ‘yan takarar shugaban kasa da suka yi nasarar lashe zaben su tare da jaddada muhimmancin zabar mata a matsayin abokan takararsu.
A cewarta, hakan zai karfafawa matan karkara da na birni kwarin guiwa da su fito fili su kada kuri’a ga duk wani dan takarar da ya zabi mace a matsayin mataimakiyarsa a zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Ta lura cewa rawar da mata ke takawa a siyasar Najeriya na da matukar fa’ida, don haka akwai bukatar dukkan masu neman shugabancin kasar nan da su zabi Mata a matsayin mataimaka.
Hakazalika ta shawarci duk ’yan takarar gwamna da suka ci zaben fidda gwani, wadanda har yanzu ba su zabi wanda za su zaba ba, da su zabi mata don samun nasara.
Ta kara da cewa shigar mata cikin harkokin siyasa yana haifar da ci gaba mai ma’ana ga dimokuradiyya, gami da biyan bukatun ‘yan kasa, kara hadin gwiwa tsakanin Jam’iyyu da kabilai, da karin zaman lafiya da ci gaba.
Ta yi nuni da cewa duk wani duk wani dan takara Namiji da ya zabi mace a matsayin abokiyar takararsa zai samu damar nasarar lashe zaben cikin sauki.
Shugabar ta kara da jaddada cewa yin hakan zai kara fahimta, gudummuwa da kuma fa’ida ga al’ummomin karkara, musamman mata, kan yadda ake tafiyar da tsarin samar da al’umma ta jinsi a matsayin wata hanya ta kara inganta tsarin jagoranci da ‘yan kasa.
Ramatu wacce ta ke kwararriya ce a fannin yaki da tashe-tashen hankula kuma jakadiyar zaman lafiya, ta ce Mata suna nuna salon shugabanci a siyasa ta hanyar yin aiki a sassan Jam’iyyu ta hanyar jiga-jigan mata na ‘yan majalisar dokoki, har ma a wuraren da ake fama da rikicin siyasa da kuma fafutukar tabbatar da daidaiton jinsi, kamar kawar da matsalar jinsi, tashin hankali, hutun iyaye da kula da yara, fansho, dokokin daidaiton jinsi, da sake fasalin zabe.
Ta yi kira ga dukkan kungiyoyin farar hula na Jihohi 36 na Najeriya da ke inganta mulkin Dimokaradiyya mai dorewa, da su jawo hankalin duk dan takarar shugaban kasa da ya zabi Mace a matsayin mataimakiyarsa a zaben shekarar 2023.
Yayin da suke kira ga dukkan ma’aikatar harkokin mata, kungiyoyin mata, kungiyoyi masu zaman kansu masu yada da’awar gwamnatin dimokaradiyya, sun yi kira ga duk masu neman shugabancin kasar da su zabi mata a matsayin abokan takararsu.
Hakazalika Hajiya Amina Marafa Ibrahim, shugabar gidauniyar mata ta Najeriya ta ce, hakika lokaci ya yi da masu neman shugabancin kasar za su fara tunanin neman mata ‘yan takara a matsayin mataimaka domin ‘yar takarar mace na da alfanu da dama da kuma samun damar lashe zaben cikin nasara.
Ta ce duk dan takarar da ya zabi mace daga kowane yanki, to ko shakka babu zai yi nasara a zaben saboda mata sun fi maza hadin kai.
Amina ta bukaci daukacin mata da su marawa duk wani dan takarar da ya zabi mace a matsayin mataimakiyarsa a zaben shekarar 2023 mai zuwa.