Za’a a fara koyar da harsunan Ijaw, Faransanci, da Sinanci a makarantun a jihar Bayelsa

0
91

Daga Maryam Umar Abdullahi

Gwamnatin Bayelsa ta ce za ta ba da fifiko kan koyo da koyar da harsunan Ijaw, da Faransanci, da kuma Sinanci a makarantun gwamnati a jihar.
Mataimakin gwamnan jihar, Mr. Lawrence Ewhrudjakpo ya bayyana a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Doubara Atasi, ya fitar a jiya Alhamis cewa, ƙaruwar tasirin tattalin arziƙin ƙasar China a harkokin duniya a matsayinta na babbar jigo a harkokin cinikayya da cinikayyar duniya, ya nuna kamatar tabbatar da shigar da ƙarshen ƙasar China a cikin manhajar karatu.

KU KUMA KARANTA: Firaiministan Nijar, Lamine Zeine, ya caccaki ECOWAS  kan yin zagon ƙasa

Ewhrudjakpo ya bayyana cewa, gwamnati za ta fi maida hankali kan harsunan ne domin, baya ga muhimman darussa na kimiyya, harsunan za su taimaka wajen samar da yaran da za su ci gajiyar damar sana’ar da waɗannan darussa ke bayarwa a nan gaba.

Ana magana da harshen Ijaw ne a yankin Niger-Delta da ya ƙunshi jihohin Delta, Bayelsa da kuma Cross Rivers. Akwai kuma waɗannan suke harshen da ake ƙira “Arogbo-Ijaw” a jihar Ondo.

A shekarun nan, masana na jadada buƙatar ganin gwamnatoci sun ɗauki matakan raya al’adu da harsuna da ake gani aka kara watsi da su sabili da ci gaba na zamani.

Leave a Reply