Za mu shiga zaɓen ƙananan hukumomi a Yobe — Jam’iyyun Adawa

0
91

Mun shirya tsaf domin shiga wannan zaɓe amma kuma muna sara ne muna duba bakin gatarinmu.

A yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin a ranar Asabar ta ƙarshen wannan wata na Mayu a Jihar Yobe, wasu shugabannin jam’iyyun adawa da ke jihar da suka haɗa da Jam’iyyar NNPP da PDP da AD da PDM sun bayyana shirinsu na shiga wannan zaɓe matuƙar za a ba su damar shiga takarar ba tare da an yi musu ƙwange ba.

Shugaban Jam’iyyar NNPP a Jihar Yobe, Alhaji Yakubu Shehu Damagum ya bayyana cewa, jam’iyyarsu ta NNPP a Jihar Yobe ta shirya tsaf don shiga zaɓen ƙananan hukumomin matuƙar Hukumar Zaɓe ta Jihar Yobe ta amince ta sayar musu da fom ɗin tsayawa takara.

Shugaban ya ce, Jam’iyyar NNPP ba ta wata tantama a kan shiga zaɓen, kamar yadda wasu ke cewa jam’iyyun adawa a jihar ba za su shiga zaɓen ba, inda ya fito ƙarara ya ƙaryata wannan magana.

Ya ƙara da cewar, babban abin da ke gabansu shi ne samun fom ɗin tsayawa takarar daga Hukumar Zaɓen jihar da kuma samun ainihin ’yan takarar da ke da sha’awar tsayawa takarar.

Ya bayyana cewa domin kuwa ya zuwa yanzun ɗan takara ɗaya tak suka samu na kansila daga Ƙaramar Hukumar Karasuwa, wanda shi kaɗai ne ya zuwa yanzu ya fito ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takara a duk Jihar Yobe, amma ba su san nan gaba.

Shugaban na NNPP ya ƙara da cewar, tuni Jam’iyyarsu ta NNPP ta tura takardarsu zuwa Hukumar zaɓe ta Jihar Yobe domin bayyana shirinsu na shiga zaɓen.

Shi ma Shugaban Jam’iyyar AD, Malam Habu Doro Potiskum bayyana wa Aminiya matsayarsu a kan cewa, su ma a shirye suke su shiga cikin wannan zaɓe na ƙananan hukumomi a Jihar ta Yobe, amma kuma suna sara ne suna duba bakin gatarinsu, domin ba zai yiwu a ba su ga ana aikata ba daidai ba kuma su zuba ido, kasancewar akwai amanar al’umma a kansu.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Yobe za ta mayar da kwale-kwalen Dufuna mai shekaru 8,000 zuwa cibiyar yawon buɗe ido

Ya ce, suna sane da cewar kai da kaya duk mallakar wuya ne, ma’ana da Hukumar Zaɓen jihar da ma’aikatanta duk mallakin Gwamnatin Jihar Yobe ne, inda ba za su taɓa yarda ’yan takararsu a kowane mataki su faɗi zaɓe ba, wanda hakan ke nuna cewar, in jam’iyyun adawa suka shiga ma, sun san yadda sakamakon zaɓen zai kasance.

Game da ko jam’iyyarsu tana da ’yan takara, sai shugaban ya bayyana cewa, zuwa yanzu ba su da ɗan takara ko da guda, wanda a ganinsa hakan ba ya rasa nasaba da tunanin da jama’a ke yi cewar, idan mutum ya fito ma bata lokacinsa da kudinsa kawai zai yi.

Ya ce kasancewarsu ’yan jam’iyyar adawa suna ganin cewa duk wanda ya fito takara ba lallai ba ne ya ci zaɓen, komai kuwa yawan jama’arsa, domin kuwa Hukumar Zaɓe ta jihar ita za ta shirya zaɓen kamar yadda kowace jiha ke yi.

A tattaunawarsa da menema labarai kuwa da Shugaban Jam’iyyar PDM a Jihar ta Yobe dangane da yiwuwar shigar jam’iyyar zaɓen ya ce, zuwa yanzu dai kam ba su yanke shawarar komai ba a kan yiwuwar shiga zaben ko kuma akasin hakan, amma za su sanar da matsayarsu nan gaba kaɗan.

A nasa ɓangaren, Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Yobe, Sanata Umar El-Gash ya ce, shakka babu jam’iyyarsu za ta shiga zaɓen kuma za a fafata da ita, fata dai kawai shi ne a yi adalci.

Leave a Reply