Za a tsayar da ranar fara ƙidayar jama’a da gidaje a Najeriya

0
283

Gwamnatin Tarayya ta ce za a fara aikin ƙidayar jama’a da gidaje na 2023 nan da watanni kaɗan dake tafe.

Wani memba a kwamitin yaɗa labarai da bayar da shawarwari kan ƙidayar yawan jama’a da gidaje na ƙasa na shekarar 2023, Dakta Garba Abari, ya tabbatar da haka ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce aikin na kwanaki uku zai fara ne nan da watanni kaɗan masu zuwa, sannan kuma za a kwashe kwanaki ne ana gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

KU KUMA KARANTA: Kimanin Yara Miliyan 13 Ne Ba Sa Zuwa Makaranta A Najeriya – UN

Abari, wanda shi ne babban Darakta na hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA), ya bayyana cewa, aikin ƙidayar zai ƙirga kowanne mutum da gida a lungu da sako a faɗin ƙasar nan.

Leave a Reply