Za a sake zaɓe a mazaɓar Ado Doguwa

Hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC ta ce ba wanda ya yi nasara a zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu na kujerar majalisar wakilai ta tarayya ta mazaɓar Doguwa da Tudunwada a jihar Kano.

A yau Laraba ne jami’in bayyana sakamakon zaɓen, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, ya sanar da haka, tare da cewa za a sake zaɓen a wasu runfuna 13.

KU KUMA KARANTA: INEC ta cire sunan Doguwa daga jerin zaɓaɓɓun ‘yan majalisun tarayya

Tun da farko an bayyana shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan ta Najeriya, Alhassan Ado Doguwa, a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

Sai dai kuma bayan da hukumar zaɓen ta fitar da jerin sunayen waɗanda suka yi nasara a zaɓukan majalisun tarayya da aka yi ranar, ba ta sanya sunansa ba a don haka ba ta ba shi takardar shedar cin zaɓen ba.
INEC ta ce an bayyana sunanasa ne a matsayin wanda ya yi nasara a bisa tilastawa.

Wannan ya biyo bayan kama Ado Doguwan bisa zargin hannu a tashin hankalin da aka yi a mazaɓar a lokacin tattara sakamkon zaɓen.


Comments

One response to “Za a sake zaɓe a mazaɓar Ado Doguwa”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Za a sake zaɓe a mazaɓar Ado Doguwa […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *