Za a rataye matashin da ya kashe matar babansa a Kano

0
266

A ranar Alhamis ne wata babbar kotu a Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Sagiru Abdullahi mai shekaru 29 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin daɓa wa kishiyar mahaifiyarsa Zainab Dan’azumi mai shekaru 55 wuƙa lamarin da yayi sanadiyar mutuwarta.

A baya dai kotun ta tsare Abdullahi ɗan unguwar Kurmawa da ke cikin birnin Kano, bisa tuhumarsa da laifin kisan kai.
Mai shari’a Aisha Mahmoud ta bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da shari’ar ba tare da wata shakka ba, inda ta kuma yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin kisa.

Tun da farko lauya mai shigar da ƙara, Tijjani Ibrahim, ya shaida wa kotun cewa Abdullahi ya aikata laifin ne a watan Yunin 2014 a unguwar Kurmawa, ya ce wanda ake ƙara ya sari matar babansa da adda a guri da dama a jikinta wanda hakan ya kai ga mutuwar ta a ranar.

“An garzaya da wadda aka kashe zuwa asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda likita ya tabbatar da rasuwar ta,” inji shi.

Ibrahim ya gabatar da shaidu biyar don tabbatar da tuhumar da ake yi wa Abdullahi wanda ya musanta aikata laifin. Abdullahi ya gabatar da shedu huɗu don su kare shi.

Leave a Reply