Za a kori ƴan ‘KEKE-NAPEP daga garin Abuja

0
491

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya ce daga watan Disamba sabbin motocin ɗaukar mutane a kwaryar birnin Abuja za su fara aiki

Alfijir Labarai ta rawaito ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce daga watan Disamba mai kamawa za a haramta ayyukan baburan KEKE-NAPEP a garin Abuja.

Wike ya ce shirye-shirye sun yi nisa domin fito da sabbin motocin ɗaukar mutane a kwaryar birnin Abuja daga wata mai zuwan.

Ya ce da zarar motocin gwamnatin sun fara aiki za a buƙaci masu KEKE-NAPEP su koma ƙauyukan Abuja da aiki.

KU KUMA KARANTA: Wike ya tattauna da makiyaya, da masu sana’ar babura a birnin Abuja

“Na san yanzu matuka KEKE-NAPEP za su fara cewa an toshe musu hanyar neman kuɗi, to amma dole mu dakatar da su domin inganta birnin Abuja, da samar da cikakken tsaro a birnin,” in ji ministan.

Wike ya bayyana hakan ne ranar talata, lokacin da yake ganawa ta musamman da masu tsara taswira da gina gidaje a Abuja, inda ya ce hakan zai rage matsalar tsaro a birnin.

Ina tabbatar muku idan motocin mu suka fara aiki matsalar kwace a cikin motocin haya za ta kau.

“Motocinmu za su rika zirga-zirga ne a hanyoyin Maitama, Asokoro da sauran sassan kwaryar birnin Abuja” inji Ministan Abuja.

Leave a Reply