Za a daina amfani da tsoffin kuɗaɗen Najeriya a watan Janairu 2023

2
499

A ranar Laraba 26 ga watan Oktoban 2022 ne, Babban Bankin Najeriya ya sanar cewa zai sauya fasalin takardun manyan kuɗin ƙasar daga naira 200 zuwa sama.

Gwamnan bankin, Godwin Emefiele ya ce za su yi hakan ne bisa buƙatar gwamnatin tarayya da kuma amincewar Shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari inda matakin zai shafi takardar naira 200 da naira 500 da kuma naira 1000.

Bankin ya ce za a yi wannan sauyi ne domin rage yawan kuɗin da ke yawo a hannun jama’a da rage hauhawar farashi da kuma magance yin jabunsu.

A dangane da hakan ne bankin ya bukaci masu kuɗi a hannu su mayar da su bankuna cikin ƙasa da kwana 50.

Haka kuma CBN, ya ce ce sabbin kuɗaɗen da za a samar za su fara yawo a hannun mutane daga ranar 15 ga watan Disambar 2022. Ya ƙara bayani da cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗaɗen har nan da ranar 31 ga watan Janairun 2023.

Bayan wa’adin da bankin ya sa na 31 ga watan Janairun sabuwar shekara, mutane ba za su iya amfani da tsofaffin takardun kuɗaɗen ba kuma.

A bayanan da bankin ya bayar ya ce, dukkanin bankunan da ke da waɗannan takardun kuɗi a yanzu suna iya fara mayar da su CBN ba tare da ɓata wani lokaci ba.

Gwamnan bankin ya ce, duk bankin da ya fara kaiwa shi za a fara bai wa sabbin takardun.Ya shawarci jama’a masu mu’amulla da bankuna waɗanda suke da kuɗaɗen a hannunsu da su fara kaiwa asusun ajiyarsu a bankunan domin a samu damar sauya su da wuri.

A sakamakon matakin, ana sa ran dukkanin bankuna su bar cibiyoyinsu na tattara kuɗaɗe a bude daga Litinin zuwa Asabar, saboda wannan shi ne zai bayar da dama ga jama’a su mayar da kuɗaɗen a kan lokaci.

Domin hanzarta sauyin, Babban Bankin na Najeriya ya dakatar da cajin kuɗin da ake biya na ajiye kuɗaɗe a bankuna.Amma kuma sanarwar ta ce idan yawan kuɗin ya wuce ₦150,000 za a biya caji.

2 COMMENTS

Leave a Reply