Zaɓen 2023: Za mu magance barazanar siyan ƙuri’u – INEC

Hukumar zabe ta INEC ta yi alƙawarin magance barazanar sayen ƙuri’u a zaɓen 2023.

Babban jami’in hukumar, Festus Okoye ne ya bayyana haka yayin wani tattaunawa kan zaɓen 2023 mai taken, “Me ke kawo kyakkyawan zaɓe a Najeriya,” inda ya ce hukumar za ta tura jami’an tsaro cikin sirri a ranar zaɓe.

KU KUMA KARANTA: Kada jam’iyyu su kuskura su karɓi tallafin kuɗi daga ƙasashen waje – INEC

Ya nanata ƙudurin hukumar na gudanar da sahihin zaɓe na gaskiya da adalci ga ɗaukacin ‘yan Najeriya tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

Ya ƙara da cewa “za mu tabbatar da cewa babu wanda zai shiga wurin zaɓe da wayar salula da za ta iya ɗaukar hoto”.

A cewar kwamishinan INEC, hukumar zaɓe za ta ci gaba da horar da ma’aikatan ta wajen ganin an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *