A yau litinin ne Hukumar Hisbah ta jihar Kano za ta yi zamanta da ’yan Kannywood da ta gayyata zuwa ofishinta.
Gayyatar da Hisba ta yi wa daraktoci da jarumai da furodusoshi ya tayar da ƙura, inda wasu daga cikin ’yan masana’antar suka bayyana takaici bisa abin da suka ƙira ƙaskanci a yadda suka ji sanarwar gayyatar Hisbar ta gidan rediyo.
Sai dai wata majiya a Hukumar Hisbah ta jihar Kano, wadda ta ce ba da ta izinin yin magana a hukumance, ta tabbatar wa Aminiya cewa hukumar ta aike wa ’yan Kannywood takardar gayyata zuwa zaman da ta shirya yi da su.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Babban Kwamandan Hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa game da batun, amma ya shaida masa cewa yau za su yi zama da ’yan masana’antar ta Kannywood da aka gayyata.
KU KUMA KARANTA: Bayan ganawa da ’yan TikTok, Hisbah ta gayyaci ’yan Kannywood
Gayyatar wadda hukumar Hisbah ta ce ba ta shafi mawaka ba ne, ta zo ne bayan a makon jiya hukumar ta yi wani zama da ’yan TikTok a shirinta na ganin sun daina yaɗa abubuwa marasa kan gado da suke yi a soshiyal midiya.
A yayin zaman na Hisbah da ’yan TikTok, ta gabatar musu da tayin ɗaukar nauyin karatu ko aure ga masu buƙata a cikinsu, ko ma ta ba su jari.
Wannan na daga cikin shirin da hukumar ta ƙaddamar da sunan Operation Kawar da Baɗala, da nufin kawar da ayyukan assha.
In zaku tuna, Neptune Hausa ta kawo muku rahoton cewa, Shugaban ƙungiyar ’yan Kannywood, Alhassan Kwalle, ya ce ba su ji daɗin gayyatar ba, kasancewa ba ta zo musu ta hannun ƙungiyarsu ko ta hannun hukumar tace fina-finai ta jihar ba.
Ahassan Kwalle ya ce ba karon farko ke nan da ƙungiyar za ta yi zama da Hisbah, kuma ba da wannan sigar ta saba gayyatar su ba.
Ya ce a shirye suke su amsa ƙiran da hukumar ta yi musu, inda ya bayyana bukatar ta gyara kuskuren da ta yi.