‘Yan shi’a sun yi muzaharar ƙudus a sassan arewacin Najeriya

0
181

‘Yan ƙungiyar Shi’a almajiran Shaikh Ibraheem El Zakzaky sun gudanar da zanga-zangar marawa Falasɗinawa baya kan yaƙin Gaza a sassa daban-daban na arewacin Najeriya.
Zanga-zangar mai taken ranar ƘUDUS, ‘yansanda sun auka mata inda suka buɗe musu wuta haka siddan a birnin Kaduna.

‘Yan Shi’a maza da mata riƙe da kwalaye na adawa da matakan Isra’ila kan Gaza sun fito kan tituna da gefen babban masallacin Abuja suna nuna buƙatar dakatar da yaƙi a Gaza. A ko’ina a faɗin duniya an gudanar da irin wannan zanga-zanga, ciki har da Ingila da Amurka, amma babu inda aka samu tashin hankali, sai a Kaduna da ‘yansanda suka buɗe musu wuta.

A Katsina jagoran Harkar Musulunci ƙarƙashin Shaikh Zakzaky, wato Shaikh Yakubu Yahaya, ya ce iya matakin muzaharar za su iya ɗauka don mara baya ga Falasɗinawa.

KU KUMA KARANTA:Ƙasashen Ghana da Kenya sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa

A tarihi dai shi kansa shugaban na Harkar Musulunci a Najeriya, Shaikh Ibraheem El Zakzaky ya ɓullo da ranar ta ƘUDUS a Najeriya don nuna goyon baya ga raunanan al’ummar Falasɗinu, wanda ya nuna hakan taron ba wai na iya ‘yan Shi’a ne kawai ba, na duk mai tausaya wa al’ummar Falasɗinu ne, musulmi ya ke ko kirista. Wanda kowa shaida ne na irin kisan ta’addancin Isra’ila ke yi a Gaza na kashe mata da ƙananan yara da tauye musu haƙƙi.

Ya ce “ga dukkan alamu mu a nan ƙasar mutane suka riƙa ɗauka tamkar al’amarin Ƙudus wani abu ne da ya shafi Larabawa ko ya shafi al’ummar musulmi ko ya shafi ƙasashe biyu Falasɗinu da Isra’ila, amma al’amarin ya wuce hakanan, al’amari da ya shafi bil’adama da duk mai mutunci da son gaskiya da amana. “

Mai Bishara a Kaduna Pastor Yohanna YD Buru na daga masu marawa tarukan ƘUDUS baya, inda ya ce “maganar Ƙudus ba ƙaramin waje ba ne ga addinai guda uku, na farko addinin Yahudu, addinin Kirista da kuma addinin Musulunci. In kuma an koma ga addinin Musulunci in an bi diddigin abun sosai to ‘yan Shi’a sun fi ɗaukar zurfin maganar Ƙudus sosai kamar yanda Yahudawa ke ɗauka, shi ya sa zafin ya kai ga wannan matsayin.”

Leave a Reply