‘Yan sanda sun kama ɓarayin wayar lantarki

0
467

Jami’an hukumar ‘yan sanda ta kar-ta-kwana wato rundunar RRS a takaice, sun cafke wasu ɓarayin wayoyin lantarki guda biyu a sassa daban-daban na Legas.

A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas, SO Benjamin Hundai an kama waɗanda ake zargin, da suka haɗarda Akpan Fortune mai shekaru 28 da Stanley Umebuane mai shekaru 24 a Ikeja da Ikoyi a ranar Lahadi, 6 ga Nuwamba, 2022.

An kama Fortune ne da safe a Acme Crescent da ke Agidingbi a Ikeja bayan da ya shiga tare da lalata igiyoyin sadarwa da janareta a wata ƙaramar tashar da ke yankin.

A nasa ɓangaren, tawagar RRS ta kama Umebuane a aikin sintiri na yau da kullun a daren Lahadi a hanyar Gerrard da ke Ikoyi a lokacin da yake tsaka da tono wayoyin wutar lantarkin.

An kama waɗanda ake zargin da wayoyin lantarkin daban-daban da aka yanka aka lalata.

Tuni dai kwamandan rundunar ta RRS, CSP Olayinka Egbeyemi ya miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka ‘yan sanda jihar Legas da ke Panti domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.

Leave a Reply