‘Yan sanda sun kama wani ɗan NYSC da ake zargi da aikata fyaɗe a Ogun

2
294

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta ce ta kama wani memba mai yi wa ƙasa hidima, (NYSC), Adebola Sodiq, bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 20 fyade. (an sakaye sunanta).

Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta ranar Asabar.

Mista Oyeyemi ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da aka kai a hedikwatar Owode Egba da ke ƙaramar hukumar Obafemi Owode a jihar ta hanyar wanda abin ya shafa.

A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan, wadda aka ke ƙara ta bayyana cewa wanda ake zargin saurayi ne a wajen ƙawarta na ƙut-da-ƙut.

KU KUMA KARANTA: An kama Limamin coci a Legas bisa zargin rashin taimakon wata mata

“Ta ce ya zo gidanta inda take zaune tare da abokan aikinta a ranar 9 ga Mayu kuma ya neme ta da ta bi shi zuwa wata junction don saya mata kyauta don murnar zagayowar ranar haihuwarta.

“Ta bayyana cewa a matsayinta na abokiyar budurwar wanda ake zargin, ba ta da dalilin zargin wani wasa mara kyau, don haka ta bi shi.

“Amma yayin da suke tafiya, wanda ake zargin ya buƙaci ta bi shi har harabar makarantar da yake hidimar ƙasa, domin ɗauko jakarsa. “Da isa harabar makarantar da ke ƙauyen Agbajege, wanda ake zargin ya ja ta da ƙarfi zuwa ɗakinsa inda Sadiq ya mata fyaɗe da ƙarfi ba bisa sonta ba, duk da roƙon da ta yi na masa na kar ya yi,” inji shi.

Mista Oyeyemi ya bayyana cewa da samun rahoton, jami’in ‘yan sanda na shiyya (DPO), reshen Owode Egba, Olasunkanmi Popoola, ya bayar da umarnin kama Sodiq.

Ya ƙara da cewa da ake yi masa tambayoyi ya amsa laifinsa amma ya ce bai san abin da ya same shi ba.

Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa ‘yan sandan sun kai wanda aka yi wa fyaɗen zuwa babban asibitin Owode Egba domin yi mata magani.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, Olanrewaju Oladimeji, ya bayar da umarnin a miƙa Sodiq zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da shi gaban ƙuliya.

2 COMMENTS

Leave a Reply