Yan Najeriya fiye da 300 ne suka mutu sanadin ambaliya a bana

1
288

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Hukumomi a Najeriya sun ce mutane sama da 300 ne suka mutu, wasu fiye da 100,000 suka rabu da muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa a fadin kasar tun daga watan Yuli.

Ambaliyar ruwan ta kuma lalata gidaje da gonaki masu tarin yawa, a halin da ake ciki Najeriya tana fama da mummunar ambaliyar ruwa mafi muni da aka taɓa

gani a cikin ‘yan shekaru, hukumomi sun ce jiha 29 cikin 36 na Najeriya ne ambaliyar ruwan ta shafa.

Ambaliyar tana faruwa ne sakamakon mamakon ruwan sama da kuma sakin madatsun ruwan da suka tumbatsa da hukumomi a cikin Najeriya da ma Kamaru mai makwabtaka ke yi. Koguna sun ciko.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta yi gargadin cewa ƙarin ambaliyar ruwa tana nan tafe cikin ‘yan makonni. Ta kuma buƙaci gwamnatocin jihohi su taimaka su kwashe mutanen da ke zaune a yankuna masu yiwuwar samun ambaliyar ruwa.

Shugaban hukumar NEMA, Ahmed Mustapha Habib, ya ce sun tura karin jami’an kai dauki da kayan aiki don taimakawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa, inda ya bayyana lamarin da cewa yana “cike da kalubale”.

Ƙasashen Afirka da dama ne ke fama da ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ba a saba gani ba sau da yawa kuma yana haddasa mummunar ambaliya.

Kwararru na dora wani bangare na alhakin ga illar sauyin yanayi. Haka zalika, an yi imani rashin ingantattun ababen more rayuwa da rashin matakan takaita ambaliya na ba da gudunmawa wajen haifar da gagarumar asara.

1 COMMENT

Leave a Reply