‘Yan kwamitin tsaron zaɓe sun gana a Abuja

0
308

Gabanin zaɓen gwamna kwamitin tuntuɓa tsakanin hukumomin tsaro kan harkokin zaɓe sun yi taro a hedikwatar hukumar zaɓe mai zaman kanta da ke Abuja a shirye-shiryen gudanar da zaɓukan gwamnoni da na majalisun jihohi.

Hotunan taron, da kuma wata sanarwa ta shafin Twitter na INEC a ranar talata sun tabbatar da hakan, haka zalika shugaban hukumar ta INEC, Mahmood Yakubu, a wata sanarwa da ya fitar, ya buƙaci jam’iyyun siyasa da su jawo hankalin magoya bayansu da kada su yi tashe-tashen hankula a lokacin zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Jihar Kwara Zai Jagoranci Kwamitin Mutane 8 Domin Duba Batun Zaben Shiyya A APC

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Kwamitin tuntuba tsakanin hukumomin tsaro kan harkokin zaɓe yana gudana ne a hedikwatar INEC dake Abuja.

Zaɓen gwamnoni/majalisun jihohi da aka shirya yi a ranar 18 ga watan Maris na kan gaba. “Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi kira ga jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da magoya bayansu da su kalli zabe a matsayin takara, ba yaki ba, kuma su guji tashe-tashen hankula da ka iya kawo cikas ga zaɓen ko kuma kawo cikas ga tsaron jami’anmu, masu sa ido, kafafen yaɗa labarai da kuma masu ba da sabis.”

Leave a Reply