‘Yan bindiga sun sace mahalarta ɗaurin aure 35 a Najeriya

0
197

Daga Maryam Umar Abdullahi

Aƙalla mata 35 ne suka ɓace bayan da masu garkuwa da mutane suka kama waɗansu mata da suka dawo daga wani ɗaurin aure a arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda jami’ai suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a ranar Litinin ɗin nan.

Satar jama’a da aka yi a jihar Katsina shi ne mafi girma a cikin jerin sace-sacen da aka yi a baya-bayan nan a ƙasar da ta fi kowacce yawan jama’a a Afirka.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Abubakar Aliyu ya ce ‘yan bindiga sun yi kwanton ɓauna ne tare da yin garkuwa da mata kimanin 35 da suke dawowa daga ɗaurin auren a unguwar Sabuwa a daren ranar Alhamis.

Kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Nasiru Muaz ya bayar da adadin da ya fi haka, inda ya ce sama da mutane 50 ne aka kama a hanyar komawa ƙauyen Damari bayan sun raka amarya gidan ango.

“Jami’ai sun ziyarci ƙauyen kuma an gaya musu cewa an ɗauke mutane 53,” in ji shi.

Yana da matuƙar haɗari ga ayarin motocin da ke ɗauke da amarya da ƙawayenta su fita kai amarya cikin duhu a cikin irin wannan wurin da ke fama da aika-aikan ‘yan fashin yayin da suke kuma waƙa.

Kwamishinan ya buƙaci mazauna yankin da su guji yin tafiye-tafiye da dare sannan ya ce jami’an tsaro na ƙoƙarin ganowa da kuɓutar da mutanen da aka kama.

KU KUMA KARANTA:Amurka ta ci tarar kamfanin ƙera motocin lantarki na Tesla dala miliyan ɗaya da rabi

Satar mutane don neman kuɗin fansa babbar matsala ce a Najeriya, inda ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke kai hari kan manyan tituna, gidaje, har ma da sace yara a makarantu.

A farkon shekarar nan ne wasu masu aikata laifuka suka sace wasu ‘yan mata mata biyar a kusa da babban birnin tarayya Abuja, inda suka kashe ɗaya bayan da wa’adin kuɗin fansa ya cika, lamarin da ya janyo cece-kuce a ƙasar.

A makon da ya gabata ne wasu masu garkuwa da mutane suka kai hari kan wata motar bas a Najeriya tare da sace yara biyar da malamansu a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin ƙasar.

An kuma kashe wasu sarakunan gargajiya biyu a wani hari na daban a jihar a ranar Litinin da ta gabata, yayin da wasu ‘yan bindiga suka harbe wani sarkin gargajiya tare da yin garkuwa da matarsa a jihar Kwara a ranar Alhamis.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau karagar mulki a bara yana mai alƙawarin magance matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Wani Kamfanin tuntuɓa mai zaman kansa da ke ba da rahotannin harkokin tsaro “SBM Intelligence” ya ce bisa ga rahoton da ya tattara, mutane 3,964 aka sace a Najeriya tun lokacin da Tinubu ya hau mulki a watan Mayu.

Leave a Reply