‘Yan bindiga sun sace ɗaliban Jami’ar jihar Nasarawa

Daga Ibraheem El-Tafseer

‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da ɗalibai huɗu na jami’ar jihar Nasarawa da ke garin Keffi.

Bayanai sun nuna cewa an sace ɗaliban ne ranar Talata a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai samame a gidajen kwanansu da ke Anguwar Kare, a ƙaramar hukumar Keffi.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar da lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho.

Ya ce da sanyin safiyar Talata ne rundunar ‘yan sanda a jihar ta samu ƙiran gaggawa cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani gida a Anguwar Kare.

“Rundunar tana sane da sace mutanen da aka yi da misalin ƙarfe 12:55 na dare yayin da aka samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka mamaye wani gida da ke Anguwar Kare, Keffi,” inji Nansel.

Ƙoƙarin da aka yi na bin sawun waɗanda suka aikata laifin ya ci tura amma an fara farauta domin kuɓutar da ɗaliban, in ji kakakin ‘yan sandan.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *