Yan Bindiga Sun Kashe Ma’aikata 36 A Jihar Kaduna – Yan Kwadago

0
338

Daga; Mustapha Imrana Abdullahi.

SHUGABAN kungiyar kwadago (NLC), reshen Jihar Kaduna, kwamared Ayuba Magaji Suleiman ya bayyana cewa ma’aikata mutum 36 ne suka rasa rayukansu sakamakon matsalar yan bindiga a Jihar.

Sakamakon hakan ne ya sa a wajen taron bikin yayan kungiyar kwadagon domin murnar ranar bikin ma’aikata ta duniya aka yi shuru na minti daya domin tunawa da wadanda suka rasu sakamakon matsalar rashin tsaro da kuma wadansu tsauraran yanayin da aka shiga.

Ayuba Magaji wanda ke magana a wajen taron ranar ma’aikata ta shekarar 2022 a babban filin wasa na ABS da ke Kaduna ranar Lahadi ya yi kira ga ma’aikata da kowa ya tabbatar ya mallaki katin zabe domin fitar da duk wani dan siyasa da ba zai kare miradunsu ba.

Shugaban na kungiyar kwadago ya kuma bukaci yayan kungiyar da su shiga a dama da su a cikin harkokin siyasa gadan gadan a madadin su tsaya a matsayin wadanda suke a kan Katanga.

Ya kuma bayyana damuwarsa da halin da yan fansho suke ciki musamman ma irin yadda ake samun saukin biyan kudin yan fansho da kudin alawus alawus da kuma yadda ake tsawaita batun tantance su kafin a tabbatar da an biyasu Hakkinsu kamar yadda yake a dokar aiki.

Ayuba Magaji ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa irin yadda take gudanar da aikin gine ginen tituna da sauransu musamman a garuruwan Kaduna Kafanchan da Zariya.

Sai dai ya ce samar da shugabanci nagari ya wuce irin yadda ake yin aikin a halin yanzu don haka ake bukatar a yi aiki sosai ta fuskar shigar da al’umma a cikin tafiyar da Gwamnati, yi wa kowa adalci da doka da oda tare da samun dai daito.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta canza irin salon tsohon yayin gudanar da dangantaka tsakanin ta da kungiyoyin kwadago wanda hakan zai ba ta damar tafiya da zamani kamar yadda ake yi a duniya ta hanyar tattaunawa da ma’aikata a duk abin da za ta gudanar a tsakaninsu.

Leave a Reply