‘Yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Minna, sun harbe masu gadi, sun kwashe kuɗi

2
383

Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a ranar talata sun kai hari fadar Sarkin Minna, Umar Faruk Bahago, inda suka yi awon gaba da wasu kuɗaɗe da ba a tantance adadinsu ba.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa ‘yan fashi da makami sun bi sawun jami’in, wanda ke dawowa daga bankin kasuwanci inda ya cire kuɗi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, sakataren masarautar Minna, Garba Musa, ya ce jami’an tsaron fadar guda biyu da suka samu raunuka harbin bindiga suna karɓar magani a babban asibitin Minna.

“Muna cikin gida tare da Mai Martaba Sarki, sai muka fara jin ƙara mai nauyi. Da farko, muna tsammanin yara ne kawai suke wasa.

Amma nan take muka ji mutane suna kururuwa ‘ɓarayi ne; ɓarayi ne’.

KU KUMA KARANTA : ‘Yan bindiga sun harbe ɗan sanda a Ibadan

Don haka na yi gaggawar fitowa na tarar a zahiri harin fashi da makami ne,” in ji Malam Musa.

“Sun harbe biyu daga cikin masu gadin fadar da ke ƙoƙarin daƙile harin. Sai dai kash an harbi ɗaya a cinyarsa yayin da ɗaya kuma aka harbe shi a ƙirji. Nan take aka garzaya da su babban asibiti.”

Ya ce ‘yan bindigar sun bi ta ƙofar gida ta biyu inda suka samu shiga inda sarkin yake zaune. “Sun yi tirela da hanya ta ƙofa ta biyu, amma ba su haura sama inda sarki yake zaune ba.

Wataƙila sun yi tunanin idan suka ci gaba zuwa wurin, za a iya kama su.

Amma sun yi nasarar kwashe kuɗaɗen ne saboda suna harbin iska har sai da suka samu hanya,” inji shi.

Malam Musa ya kuma tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka sace na masarautar ne.

Ya ƙara da cewa an sanar da ‘yan sanda lamarin, kuma sun yi alkawarin za su ɗauki matakin kamo masu laifin.

2 COMMENTS

Leave a Reply