‘Yan bindiga a Yobe sun kashe ‘yan Shi’a 3

0
35
Yan bindiga a Yobe sun kashe ‘yan Shi’a 3

‘Yan bindiga a Yobe sun kashe ‘yan Shi’a 3

Daga Ibraheem El-Tafseer

Mahara ɗauke da manyan bindigu sun kashe ‘yan Shi’a uku a makarantar Fudiyya da ke ƙaramar hukumar Geidam a jihar Yobe.

Makarantar Fudiyya na Harkar Musulunci a Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky.

Fudiyya na nan ne a unguwar Hausari da ke ƙaramar hukumar Geidam, inda maharan suka mamaye da misalin ƙarfe 3:44 na dare, wayewar ranar Juma’a.

Mahadi Asadullah ya shaida wa jaridar Neptune Prime cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne a lokacin da ɗaliban suke gudanar da ibada na Sallah a cikin Fudiyya ɗin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Kaduna sun yi garkuwa da Hakimi tare wasu mutane 5

“Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:44 na safe, a lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari makarantar Fudiyya wata fitacciyar makarantar Shi’a da ke Geidam.”

“Su (’yan bindiga) sun kai hari makarantar ne a lokacin da waɗannan matasan ke ibada suka fito da su waje suka harbe su har lahira.

“Akwai tashin hankali da damuwa a garin bayan faruwar lamarin. Jama’a sun firgita da wannan mummunan lamari,” inji shi.

Wata majiya daga rundunar ‘yan banga ta shaida wa wakilinmu cewa ‘yan ƙungiyar Shi’a uku sun mutu yayin da ɗaya ya samu raunuka.

“Ba mu san ko su wane ne (’yan bindiga) ba amma, abin da muka sani shi ne sun kashe ɗalibai uku a makarantar. Mutum ɗaya da ya yi ƙoƙarin tserewa yayin da lamarin ya faru ya samu rauni kuma an kwantar da shi a asibiti,” inji shi.

Da aka tuntubi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai bayar da cikakken bayani ba.

Wakilin Shaikh Zakzaky a garin Gaidam, Malam Kolo Gaidam ya ce “za a yi jana’izar shahidan da misalin ƙarfe 3:00 na rana, kuma za mu yi cikakken bayani kan abin da ya faru da ‘yan uwanmu”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here